Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa NLC ta ayyana gudanar da gagarumar zanga-zangar kwana biyu a ranakun 27 da 28 ga watan Fabarairu.
Shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero, ne ya bayyana haka a shalkwatar ƙungiyar a yayin wani taron gaggawa da ƙungiyar ta kira ranar Juma’ar.
- Basunu: Zuriyar Hausawa da ba sa jin Hausa a Ibadan
- An rufe SAHAD STORE kan yi wa kwastomomi zamba a Abuja
Mista Ajaero ya ce an ɗauki matakin zanga-zangar ne bayan ƙarewar wa’adin kwanaki 14 da ƙungiyar ta bai wa gwamnatin tarayya kan tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.
Ƙungiyar dai ta bai wa gwamnati wa’adin ne domin da ɓullo da wasu sauye-sauyen da za su magance matsalolin da ’yan ƙasar ke fuskanta sakamakon matsin rayuwa.
Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar Alhamis, 8 ga watan Fabarairu ne Gamayyar Kungiyoyin Ƙwadago da suka haɗa da NLC da Ƙungiyar ‘Yan Kasuwa ta Kasa (TUC) suka bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 na soma yajin aiki saboda ƙuncin rayuwa da ake fuskanta a faɗin kasar.
Tun a wancan lokacin dai wa’adin shiga yajin aikin kamar yadda sanarwar ’yan Ƙwadagon ta bayyana zai fara ne daga ranar Juma’a, 9 ga watan Fabarairu.