✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe SAHAD STORE kan yi wa kwastomomi zamba a Abuja

An dai zargi Sahad Store da kara wa kwastomomi kudin kaya fiye da farashin da ke makale a jikin kayan.

Hukumar Kare Hakkin Mai Saye Ta Gwamnatin Tarayya (FCCPC), ta rufe katafaren shagon sayar da kayayyaki na Sahad Store da ke Abuja, kan zargin su da kara wa kwastomomi farashin kaya.

Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana hanyoyin dakile matsalar karancin abinci da tsadarsa a fadin Najeriya.

Jami’an hukumar da ke kare hakkin masu saye ne suka rufe, babban shagon nan na Sahad Stores da ke yankin Area 11 a Abuja.

An dai zargin cewa masu katafaren shagon da kara wa kwastomomi kudin kaya fiye da farashin da ke makale a jikin kayan.

Shugaban hukumar, Adamu Ahmed Abdullahi ya ce wani bincike da hukumar ta gudanar kan katafaren shagon ya nuna yadda suke cutar mutane.

Ya kara da cewa shagon zai ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

“Mun fahimci cewa mutanen nan abin da suke yi yaudara ne, inda babu gaskiya dangane da farashin kayan da suke sayarwa wanda kuma hakan ya yi karo da sashe na (135) da dokar da ta hana a yaudarar abokin hulda.”

Wannan dai na zuwa ne bayan da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kokawa kan yadda farashin kayayyaki ke tashin gwauron zabi.

Hakan ne ya sanya Shugaba Tinubu gana wa da gwamnonin jihohi a ranar Alhamis , don tattauna hanyar da za a dakile tashin farashin kayayyaki da kuma magance matsalar tsaro.

Hotunan yadda jami’an hukumar suka rufe katafaren shagon: