Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) da takwararta ta ’yan kasuwa (TUC) a Jihar Filato na shirin fara yajin aikin gargadi na kwana biyar saboda rashin biyan albashi da sauran hakkokin ma’aikata.
Cikin wasikar da ta fitar ranar Alhamis mai dauke da sa hannun shugabanta na jihar, Eugene Manji, NLC ta ce ta soma neman hadin kan sauran takwarorinta a jihar don su shiga yajin aikin.
- Gwamnati ta yi watsi da mu Nakasassun Adamawa
- 2023: Ku tsumayi takarar Kirista da Kirista —Matar Tinubu
Shugaban kwamitin sulhu na hadin gwiwa (JNPSNC) reshen Filato, Mista Titus Malau, ya shaida wa NAN cewa shiga yajin aikin ya zama wajibi saboda gazawar gwamnati wajen cimma bukatun ma’aikatanta.
Ya ce matsalar albashin ma’aikata na daga cikin dalilan da suka sanya su yanke shawarar shiga yajin aikin gargadi don jan hankalin gwamnati.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ce NLC ta shirya fara yajin aikin ne ranar 11 ga Disamba da misalin karfe 12:00 na dare.
Shugabannin kungiyar sun yi kira ga ma’aikatan gwamnati a jihar da su ba da cikakken hadin kansu kan matakin.
(NAN)