Shahararren dan wasan fim din barkwanci na Kudancin Najeriya Nkem Owoh wanda aka fi sani da Ukwa ko Osuofia ya fara fim din Hausa.
dan wasan ya fito a wani fim mai suna ‘Maja’ da kamfanin Faidhat Production da ke Kano ya shirya a kauyen Mahuta da ke Jihar Kaduna da kuma Abuja.
An fara daukar fim din Kaduna inda aka kammala Lahadin da ta gabata a Abuja.
Fim din ‘Maja’ labari ne a kan Uwale (Hafsatu Sharada) da ta auri wani dan kabilar Ibo a Inugu har ta haifi Ndibuisi (Nkem Owoh), bayan mijinta ya mutu ne ‘yan uwansa suka tsangwame ta, hakan ya sanya ta dawo Arewa, ta kuma auri wani mai kudi har suka haifi Sallau (Rabilu Musa Ibro). Bayan ya rasu ne rikici ya hada da dan uwan mijinta Kabiru (Malam Dare), shi kuma yana da labarin auren da ta yi a Inugu, hakan ya sanya ya tafi can ya kuma fada wa Ndibuisi cewa mahaifiyarsa ta auri wani mai kudi ya mutu ya bar ta da tarin dukiya.
Ba shiri ya biyo Kabiru Arewa wanda ya yi sanadiyyar da rikici ya shiga tsakaninsa da Sallau, karshe Ndibuisi ya gudu da dukiyar da mahaifin Sallau ya bari. Sallau ya shiga nemansa, shi kuma Ndibuisi ya ci gaba da sharholiya. Bayan Sallau ya gano inda yake a birni ne wani sabon rikici ya balle a tsakaninsu, daga baya suka shirya.
Nkem Owoh ya ce fim din ya burge shi, kayan aikin da aka yi aiki da su ma sun kayatar da shi, “Fim din ya koyar da hadin kai, kuma zan ci gaba da yin fina-finan Hausa matukar aka neme ni, domin na yaba da irin yadda suke aiki. Ibro ya burge ni sosai.”
Ya ce: Zai zama jakadan da zai rika sanar da jama’a mutanen Arewa masu zaman lafiya da karrama jama’a ne.
A karshe ya nemi a ci gaba da hadaka tsakanin Kannywood da kuma na Nollywood, yin hakan zai sanya a gudu tare a tsira tare.
Mai kamfanin Faidhat Production, Abba Miko Yakasai ya ce fim din yana koyar da hadin kai tsakanin kabilun Najeriya musamman ma da a yanzu ake cikin mawuyacin hali.
Abdulkareem Papalaji ne ya rubuta labarin ya kuma tsara, Sadik M Mafiya ya ba da umarni, Naziru dan Hajiya ya shirya.
Sauran ‘yan wasa sun hada da Nkem Owoh (Ndibuisi), Rabilu Musa Ibro (Sallau), Maryam Jibrin Gidado (Ladiyo), Ngozi Rashida Abubakar (Ngozi), Hafsat Sharada (Uwale), Baban Chinedu (Ukechukwu), A’isha Abubakar Tsamiya (Chiboza) da sauransu.
Ba wannan ne fim na farko aka yi hadaka tsakanin jaruman Kannywood da Nollywood ba, idan ba za a manta ba dai akwai fim din ‘Oga Abuja’ da aka hada Ali Nuhu da Rabilu Musa Ibro da kuma John Okafor wanda aka fi sani da Mr. Ibu; sai kuma fim din ‘karangiya’ da aka hada Rabilu Musa Ibro da Osita Iheme da Chinedu Ikedeze da aka fi kiransu da Aki and Popo.
Nkem Owoh ya fara fitowa fim din Hausa
Shahararren dan wasan fim din barkwanci na Kudancin Najeriya Nkem Owoh wanda aka fi sani da Ukwa ko Osuofia ya fara fim din Hausa.dan wasan…
