Shugaban Kasar Nijar, Mohamed Bazoum, ya ce kasarsa ta amince ta karbi dakarun kasar Faransa da na Tarayyar Turai da suka fice daga kasar Mali don inganta tsaron iyakokin kasarsa.
Kalaman na Shugaba Bazoum na ranar Juma’a na zuwa ne kwana daya bayan dakarun Faransan da na Tarayyar Turai sun sanar da matakinsu na janyewa daga yakin da suke yi da kungiyoyi masu dauke da makamai a Yammacin yankin Sahel.
- Gwamnatin Oyo ta shirya zaman sulhu da bata-garin Jihar
- An cafke ’yan bumburutu 2 da jarka 30 na fetur a Kwara
A cewar Shugaban, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter, “Babban burinmu shi ne mu tsare kan iyakokimu da Mali, musamman yanzu da muke harsashen karuwar hare-haren kungiyoyin saboda janyewar Faransan.
“Kan iyakarmu za ta zama wata mafaka ga ’yan ta’adda, mun san za su nemi fadada ayyukansu, amma ba ma so hakan ta faru. Saboda haka, wadannan dakarun za su taimaka wajen kare mu daga su,” inji Bazoum.
Akalla dakarun Faransa 2,400 da aka jibge a kasar Mali don yaki da ’yan ta’adda da kuma wasu 900 ne ake sa ran za su fice daga kasar ta Mali nan da ‘yan watanni masu zuwa.
Kasashen Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso dai na ta kokarin ganin sun yaki ’yan ta’addan da ke dauke da makamai, wadanda suka kashe daruruwan mutane sannan suka raba miliyoyi da muhallansu.
Sai dai Shugaban wata kungiya da ta jima tana shirya zanga-zangar kin jinin Faransa a Nijar din, Maïkol Zodi, a ranar Alhamis ya ce zaman dakarun a kasarsu haramtacce ne.
“Ba za ta sabu ba, kuma ba za mu lamunta a jibge mana dakarun a kasarmu ba, idan kuma suka kuskura suka yi hakan, to ba makawa za mu dauke su a matsayin ’yan mamaya,” inji shi.