Jamhuriyar Nijar ta maido ‘yan Najeriya da suka makale a kasarta su 177 gida.
Mutanen sun sauka ne filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, da misalin 9:29 na daren Laraba.
Ministar Bayar da Agaji, Sadiya Umar Faruk ce ta tarbe su da taimakon jami’an Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC).
Kaftin Shehu Sadiq mai ritaya ne ya wakilci ministar wajen karbar mutanen da suka dawo.
A makonnin biya, Nijar ta tiso keryar wasu ‘yan Najeriya da suka shiga kasarta ta barauniyar hanya, wadanda jami’an shige da fice na Najeriya suka gurfanar a gaban kotu.
Wasu na ganin anya wannan abu da ke faruwa na iya kawo nakasu ga dankon zumince da aka kwashe shekaru masu tsawo ana yi tsakanin kasashen nan biyu ba.
Akwai dimbin ‘yan kasar ta Nijar da ke zaune a Najeriya na tsawon shekaru da ake ganin sun yi kakagida a cikin makwabciyar ta kasarsu.