Shugaban Kasa Bola Tinubu zai yi wa ’yan Najeriya jawabi da safiyar Lahadi, albarkacin cikar kasar shekara 63 da samun ’yancin kai.
Zai yi jawabin ne a cikin jerin abubuwan da aka shirya yi domin murnar zagayowar ranar.
- Kotu ta kori ƙarar NNPP, ta tabbatar da nasarar PDP a kujerar Gwamnan Taraba
- Uwa ta kama wanda ya yi garkuwa da ’yarta a wajen karbar fansa a Zariya
Kakakakin shugaban, Ajuri Ngelale, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da maraicen Asabar.
Ya ce, “A jerin abubuwan da aka shirya yi domin cikar Najeriya shekara 63 da samun ’yancin kai, Shugaban Kasa Bola Tinubu zai yi wa ’yan Najeriya jawabi ranar Lahadi, ɗaya ga watan Oktoban 2023, da misalin karfe 7:00 na safe.
“Ana shawartar kafafen yada labarai na rediyo da talabijin da su jona da gidan talabijin na kasa (NTA) da gidan rediyon tarayya domin watsa jawabin kai tsaye,” kamar yadda sanarwar ta fada.
Wannan dai shi ne jawabin ranar samun ’yancin kai na farko da Tinubu zai yi a matsayin shugaban Najeriya.