✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta kori ƙarar NNPP, ta tabbatar da nasarar PDP a kujerar Gwamnan Taraba

Kotun ta ce NNPP ta gaza gabatar da hujjojin da za su tabbatar da da’awarta

Kotun sauraron kararrakin zaben Gwamna a Jihar Taraba ta kori karar da jam’iyyar NNPP ta shigar a gabanta, sannan ta tabbatar da nasarar Agbu Kefas na jam’iyyar PDP.

Shugaban kotun Mai Shari’a G.A. Sunmonu, a lokacin da yake karanta hukuncin kotun ya ce NNPP ba ta bayar  da wata kwakkwarar shaida da za ta gamsar da kotun kan zargi rashin bin ka’idojin zabe da ta yi wa gwamna Agbu Kefas ba.

Ya kuma ce kotun ta tabbatar wa Gwamna Kefas da kujerarsa kan cewa shi ne ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris din da ya gabata.

Sauran alkalan kotun su biyu, Mai Shari’a U. Onwosi da Khadi M.N Sidi, sun goyi bayan hukuncin kotun.