Ya ce, “Mun tattauna inda aka kwana a shirin babban taron jam’iyya da abin da ya kamata a yi nan gaba domin gudanar da taron na ranar 26 ga watan Maris cikin nasara.”
An tambaye shi dalilin da ya jagoranci taron, sai ya ce, “Ni ne Mukaddashin Shugaba; Na dan jima ina aiki a matsayin riko bayan shugaba (Buni) ya yi tafiya.”
Dambarwar sallamar na zuwa ne a yayin da Buni ke duba lafiyarsa a kasar Jamus, kuma washegarin tafiyar Buhari kasar Birtaniya domin ganin likita.
A ja wa Gwamna Bello kunne
Taron sirrrin da Gwamnan Bello ya gudanar dai ya kasance wani bakon abu a hedikwatar ta APC.
Kafin yanzu,m Sakataren Kwamitin Rikon Jam’iyyar, Sanata John James, ne yake gudanar da harkoki a hedikwatar jam’iyyar bayan tafiyar da Buni ya yi.
Kafin yanzu, shi dai Gwamnan mamba ne kawai a Kwamitin Rikon Jam’iyyar APC.
Neman takara na neman tayar da fitina
Sanarwar da Nabena ya fitar ta yi zargin cewa shirin neman takarar mataimakin shugaban kasa da Bello ke yi na neman kawo kama-karya a jam’iyya.
“Kada Gwamna Bello ya wargaza APC saboda burinsa na zama mataimakin shugaban kasa ko wani abu a 2023; Shi da ire-irensa hankakin siyasa ne da ke cin diddigen jam’iyyar domin kawo kama-karya.
“Ina kira ga jagororin jam’iyya a fadin jihohi da Fadar Shugaban Kasa cewa su taka wa Gwamna Bello burki kan taron Kwamitin Zartar da yake son gudanarwa ba da sanin Mai Mala Buni ko Sakataren Kwamitin Rikon Jam’iyya ba.