✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Ni na jagorance Rabaran Simon ya shiga Musulunci – Sakataren Sarkin Hausawa

Ko ya kuka ji da wannan lamari na musuluntar Rabaran Fada Simon a Sabo Shagamu? Alal haƙiƙa wannan lamari abu ne daga Allah. Shi daman…

Ko ya kuka ji da wannan lamari na musuluntar Rabaran Fada Simon a Sabo Shagamu?

Alal haƙiƙa wannan lamari abu ne daga Allah. Shi daman wannan bawan Allah mutum ne wanda daman can na san shi, muna yin tarurruka da shi kan abin da ya shafi zaman lafiya, harkar addini da ta ƙungiyoyinmu na baƙi; wato ƙabilun da ba Yarabawa ba amma muke zaune a nan yankinsu.  Yadda lamarin ya faru shi ne, wata rana ne da sanyin safiyar Lahadi, yau kimanin wata guda ke nan, sai Rabaran Fadan ya zo gidana yana buga ƙofa. Da na ji bugun ƙofar amma ban fito ba sai mutanen da ke zaune a wajan suka faɗa masa cewa ba na fitowa sai ƙarfe 10. Daga nan ya tafi sai ya dawo, koda ya zo bayan mun gaisa sai ya ce mani ban gane shi ba ne? na ce na dai so in ɗauki kama, sai ya ce Rabaran Fada Simon Paul ne. Sai ya tambaye ni ya ake shiga Musulunci na ce masa ban gane me yake nufi ba. Sai ya ce mani shi ne yake so ya shiga musulumci. Sai na ce masa ya je ya dawo lokacin Sallar Azahar, zan kai shi masallaci wajan limamin gari. Koda ya tafi ba a jima ba sai ya sake kirana ta waya, ya ce don Allah kada in manta, da gaske yake a kan wannan lamari.

To bai iya haƙuri har lokacin Azahar ɗin ba, sai wajen sha biyun rana ya sake komowa. To a haka dai har lokacin zahar na kai shi masallaci, na yi wa liman bayani. Ya yi murna, ya ce ai ƙaruwa ce Musulmi suka samu. Nan liman ya karanta masa sharuɗɗa sannan ya karɓi Musulunci. Daga nan ya ce zai faɗa mana dalilin da ya sa ya musulunta, ya ce a lokacin da Shugaban kasa ba shi da lafiya har aka fitar da shi ƙasar waje, ƙungiyarsu ta umarce su da su yi azumi da addu’a; matuƙar har sun yi Shugaban kasa ba zai dawo da ransa ba. Sai shi ya ce masu muddin aka samu akasin haka, to zai musulunta. Haka kuwa aka yi, bayan da Allah Ya bai wa Shugaban kasa lafiya ya dawo, shi ne shi kuma ya zo ya karɓi Musulunci, ya cika alƙawarinsa, kodayake a da ya jinkirta haka har sai da ya yi mafarki da wani mutum ɗauke da babban carbi, wanda ya ce masa kada ya manta da alƙawarin da ya yi. Hakan ne ya sanya ya zo don ya cika alƙawarin.

Kuma ya tabbatar mana da cewa ya musulunta tsakaninsa da Allah. Ya ce a ba shi Alƙur’ani ya yi rantsuwa sannan ya ce yana so mu taya shi da addu’a, albarkacin wannan Alƙur’ani Allah Ya kare shi daga sharrin ’yan uwansa, domin ya san abin da ya yi ɗin nan zai fuskanci fushin ’yan uwansa da makirce-makirce amma shi bai damu ba, in ma kashe shi za su yi, to shi dai buƙatarsa ya mutu a Musulunci. Nan aka koya masa yadda ake yin wanka, alwala da dai sauransu.

Ko wane hali ya shi ga bayan da ya ƙarɓi Musuluncin?

Bayan da ya koma gida ya kira ni ta waya yake faɗa mani cewa ’yan uwansa sun ɗaure shi, sun kulle a wani ɗaki, ba su ba shi abinci ko ruwa. Sai na tambaye shi ko yana buƙatar wani taimako ne ko kuma mu sanar wa hukuma? Sai ya ce a’a mu dai taya shi da addu’a. To, bayan wani lokaci kuma sai ya kira ni yake faɗa mani cewa ’yan uwan nasa na shirin mayar da shi garinsu a Jihar Imo. To, bayan sun mayar da shi can ne sai ya kuɓuta daga wajensu, a lokacin ya kira ni ta waya yake faɗa mani, sai na tambaye shi ya za a yi ya dawo? Sai ya ce zai sayar da wayarsa ya yi kuɗin mota. Sai na ce masa kada ya sayar da wayar, in ya yi haka babu yadda za mu dinga samun labarinsa ke nan. Sai na ce ya je duk inda ya ga Hausawa a inda yake, ya haɗa ni da su zan yi masu magana su taimaka masa.

Haka kuwa aka yi, ya je unguwar wasu Hausawa a nan Imo, ya haɗa ni da su, na yi masu bayani suka kai shi masallaci aka haɗa masa kuɗi, aka sanya shi a mota ya dawo nan Shagamu. To, hankalinsa bai kwanta da nan ba, domin daman can a nan yake da zama sai ya ji tsoron ko ’yan uwan nasa za su zo su sake kama shi. Hakan ne ya sanya ya koma Asaba, inda ya sami mafaka.

Wane irin tallafi yake buƙata?

A gaskiya yana buƙatar taimakon al’ummar Musulmi, domin ya faɗa mana babban burinsa shi ne ya yi ilimin addini. To, ka ga da za a sami wasu mutane ko ƙungiyar da za su ɗauki nauyinsa ta wannan fanni to da abin ya yi kyau. Idan ka dubi yawan shekarunsa da kuma matsayinsa na Rabaran Fada wanda a da cocin da yake aiki sun ba shi gida da mota amma ya yi watsi da su, ya bar duk wata daula ya kama ga Allah; to ya kamata mutanenmu su taimaka masa, domin mu nan ba masu ƙarfi ba ne. Mun yi namu ƙoƙarin, muna fata ko daga Arewa ne ya sami tallafin yin karatu da ci gaba da gudanar da rayuwarsa, domin yana da ’yaya 6 da ’yan uwansa amma duk sun yi watsi da shi saboda ya karɓi Musulunci; yanzu shi kaɗai yake rayuwa tare da ’yan uwa Musulmi a inda ya sami mafaka. Da zai samu mafaka a Arewa, inda zai dinga samun kulawa tare da samun ilimin addini, ina ba ka tabbaci shi ma zai bai wa addinin nasa gudunmawa.

Ko a ranar 27 ga watan da ya gabata, an samu mutum 46 da suka musulunta a garin na Shagamu, a lokacin da wani Shaihin Malami Yusuf Adepoju, wanda masani ne a ilimin Baibul da addinin Musulumci, bayan ya yi wa’azi tare da muƙabala da wasu limaman Kirista a garin Shagamu, sai aka yi ta samun mutane da dama; suna zuwa suna ƙarɓar Musulunci.