✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Babiana

Babiana ta yi alƙawarin ci gaba da haɗa aure a tsakanin jaruman Tiktok.

Fitacciyar ’yar Tiktok, Hafsat Babiana, ta ce ita ce ta haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles Borno.

A wani bidiyo da Babiana ta wallafa a Tiktok, ta ce ta haɗa auren ne domin raya sunnar ma’aiki, da kuma fatan za su rufa wa juna asiri.

Sai dai, Babiana ta ce tun tafiya ba ta yi nisa ba, masoyan sun fara kai ta bango.

“Na haɗa sunnar ma’aiki ne saboda Alpha ta shigo mu samu lada, mu kuma samu ƙari a addinin Musulunci.

“Muna so ta tsundumo cikin alheri domin samun tabbarraki a ranar alƙiyama,” in ji ta.

“Amma fa G-fresh, ni ban ce ka dinga ɗaukar hoto na gwatso ba, ban kuma ce ka dinga sumbata ba a kyamera saboda kullum kana haka-haka.”

Ta ƙara da cewar, game da masu neman ba’asin ingancin lafiyar ma’auratan kuwa, Babiana ta ce garau suke, domin tana da shaidar gwajin sakamakon cuta mai karya garkuwar jiki da aka yi masoyan.

“Masu kirana suna tambayar an yi gwajin ƙanjamau, to, tabbas an yi zan kawo muku shi nan ba da daɗewa ba.”

Hakazalika, ta ce akwai wani auren ma da ta ke shirin haɗawa yanzu haka, tsakanin wasu fitattun ’yan Tiktok.

A cewarta da bidiyon da suke yaɗawa s kafar gara su yi aure, zai fi musu samun lada.

A gefe guda kuma, ta nemi shawarar masu bibiyarta kan waɗanda suke ganin dacewar ta haɗa aure a Tiktok.

Kuma ta ce idan har an dace tafiyar aka dace, za ta biya sadakin waɗanda za ta haɗa auren.

“Waɗannan aure-auren sai an yi su ko ku suna so, ko ba sa so. Domin na fahimci idan ban yi musu haka ba, wasun su haka za su zo a alakoro su koma a bati ba tare da sun yi ba,” in ji ta.