✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ni na dora Bala a Gwamna, kuma ni zan sauke shi – Tsohon Wazirin Bauchi

Sai na cire Gwamna Bala kamar yadda ya cire ni, in ji Kirfi.

Tubabben Wazirin Bauchi, Muhammadu Bello Kirfi, ya sha alwashin sai ya cire Gwamnan Jihar, Bala Mohammed, daga mukaminsa kamar yadda shi ma ya cire shi daga mukaminsa.

Kirfi ya bayyana haka ne sakamakon tube masa rawani da Masarautar Bauchi ta yi masa a matsayin Wazirin Bauchi.

Masarautar Bauchi ta tube tsohon Wazirin ne saboda abin da ta kira da rashin biyayya ga Gwamnan Jihar.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Lahadi, Kirfi ya ce, “Hanyar da na shigar da shi ofis, ta nan zai bi ya fita.

“Na dauki abin da ya faru da ni a matsayin karamin al’amari saboda wani abu na damuna a raina.

“Ina daya daga cikin wadanda suka tsaya masa ya samu Gwamna, kuma na ji takaicin abin.

“Wannan shi ne iya abin da zai iya yi, ba komai ba ne wannan saboda babu wata riba da nake samu (a matsayin Waziri) a Fadar Sarki.”

Ya ce ya taka muhimmiyar rawa a zama gwamnan da Bala ya yi a 2019, saboda a lokacin yana matukar neman goyon baya don cika burinsa na siyasa.

“Na yi dukkan mai yiwuwa wajen tabbatar da ya samu nasara a kan gwamnatin da ke dasawa da Gwamnatin Tarayya a wancan lokaci,” in ji shi.

Kazalika, Kirfi ya ce Gwamnan ya ci amanar jiga-jigan ‘yan siyasar da suka taimaka masa wajen cin zabe.

Ya ce Bala ya yi fada da kusan baki dayan wadanda suka yi ruwa da tsaki a zaben da ya lashe 2019.

“Na bar wa Allah komai, Shi ne zai yi mana shari’a kan abin da ke tsakanina da shi,” in ji shi.

Sai dai kuma, Daraktan Yada Labarai na Kwamitin Yakin Neman Zaben Gwamna na PDP a 2023, Yayanuwa Zainabari, ya ce kwamitin bai damu da barazanar ta Kirfi ba.

“A wajen jama’ar Bauchi Gwamna Mohammed ke neman a sake zabensa amma ba a wajen mutum guda ba saboda Allah ke ba da mulki ga wanda ya so,” in ji Zainabari.