Mutum 24 ne suka rasa rayukansu, yayin da 187 sun jikkata, sannan gidaje sama da 30,000 suka rushe sakamakon ambaliyar ruwa a Jihar Bauchi.
A wajen rabon kayan tallafi da ECOWAS ta raba, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar ya wakilta, ya bayyana cewa an kashe sama da dala 200,000 wajen tallafa wa magidanta 1,000 daga ƙananan hukumomi shida da suka fi shan wahala.
Kowane magidanci ya samu kyautar Naira 75,000 tare da kayan abinci.
Kayan abincin sun haɗar da shinkafa, wake, man girki, bargo, da gidan sauro.
Gwamnatin jihar ta kuma ƙara tallafawa wasu magidanta 150 masu rauni don rage musu raɗaɗin iftila’in.
Waɗanda suka ci gajiyar tallafin, sun yi wa ECOWAS, Red Cross a gwamnati jihar godiya bisa tallafin da ska ba su.
Gwamna Bala, ya ce wannan tallafin wani ɓangare ne na ƙoƙarin rage wahalar da mutane ke fuskanta sakamakon ambaliyar ruwan.
Ya yi kira ga hukumomi da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su ci gaba da tallafa wa waɗanda iftila’in ya shafa.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Bauchi, za ta ci gaba da yin aiki tare da abokan hulɗa don samar da hanyoyin da za su kare al’umma daga irin wannan iftila’in a nan gaba, ciki har da inganta tsarin gini da hana kwararar ruwa.