Kwamishinar Bunkasa Kungiyoyi, Kananan da Matsakaitan Sana’o’i ta Jihar Bauchi, Sa’adatu Bello Kirifi, ta ajiye mukaminta, bayan an sauke mahaifinta daga sarauta.
Sa’adatu Bello Kirifi ta yi murabus ne kasa da awa 24 bayan an tube wa mahaifin nata, Alhaji Muhammadu Bello Kirfi, rawaminsa na Wazirin Bauchi tare da sallamar sa daga Majalisar Masarauar a ranar Talata.
- An kama mai gyaran wuta a cikin likitocin bogi masu aiki a asibitoci fiye da 100 a Kano
- Sanatoci 3 da har yanzu ba a maye gurbinsu ba bayan watanni 9 da murabus
A takardar ajiye aikin da ta aike wa Gwamna Bala Mohammed ranar Laraba, Honorabul Sa’adatu ta ce, “Ina mika takardata ta yin murabus daga Majalisar Zartarwa da kuma kujerar Kwamishinar Bunkasa Kungiyoyi, Kanana da Matsakaitan Sana’o’i ta Jihar Bauchi, ba tare da bata lokaci ba.
“Ina godiya ga Gwamna da ya ba ni damar yi wa Jihar Bauchi aiki a gwamnatinka.”