Rahotanni a baya-bayan nan sun bayyana cewa hadimin gwamnan Kano, Murtala Gwarmai ya raba jakuna a matsayin tallafi ga wasu matasan karkara a jihar.
Daya daga cikin wanda suka ci gajiyar tallafin jakunan mai suna Mudi, ya ce shi ya bukaci a ba shi jakin saboda zai taimaka masa wajen aikinsa na dibar kasa da duwatsu.
- Hadimin Ganduje ya gwangwaje matasa da tallafin Jakuna
- Manoman auduga dubu 94 sun samu tallafi a Kano da Jigawa
“A baya jakuna suna da arha amma yanzu sun yi tsada saboda an fara safararsu zuwa kasar China.
“Marasa karfi irina ba za su iya sayensa ba, tunda aka fara safararsa ya yi tsada matuka.
“A da zaka iya sayen jaki a kan kudi kasa da N20,000, amma a yanzu ya haura 200,000”, inji Mudi.
Ya kara da cewa hadimin gwamnan ya bukaci kowane ya bayyana abin da yake so a tallafa masa da shi, wanda shi ne ya zabi a tallafa masa da jaki.
Murtala Gwarmai wanda hadimin Gwamna Abdullahi Ganduje na musamman kan harkkokin ci gaban matasa, ya tallafa wa matasa da abubuwa da dama.
Daga ciki akwai wadanda aka ba wa kudi, babura, kekuna, da kuma wanda aka ba wa jaki a matsayin nasa tallafin.