✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NFF ta yi wa ’yan wasan U-23 ruwan Naira

Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) ta biya daukacin ’yan wasan kungiyar kwallon kafa ta ’Yan kasa da Shekara 23 (U-23) da masu horar da…

Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) ta biya daukacin ’yan wasan kungiyar kwallon kafa ta ’Yan kasa da Shekara 23 (U-23) da masu horar da su basussukan da suke bin ta.
Kamar yadda kafar labaran wasanni ta theeagleonline.com ta kalato, hukumar ta biya kowane dan kwallon Dala dubu 12 wanda ya yi daidai da Naira miliyan uku yayin da aka ba Kocinsu Samson Siasia Dala dubu 24 wanda ya yi daidai da Naira miliyan 6.
Kamar yadda kasafin ya nuna, an biya kowane dan wasa Dala dubu 4 kwatankwacin Naira miliyan day ne a matsayin alawus din nasarar lashe kofin bayan sun doke Aljeriya a wasan karshe.
Sannan an ba kowane dan wasa Dala dubu 3 kwatankwacin Naira dubu 753 a matsayin alawus din doke Senegal mai masaukin baki a wasan kusa da na karshe (Semi Final).  Sannan an ba su Dala dubu 2 bayan sun doke Mali a wasan farko yayin da aka ba su Dala dubu daya saboda kunnen dokin da suka yi da kasashen Masar da Aljeriya a zagayen farko.
Sai dai wani rahoto ya ce da ’yan wasan ba su samu nasarar lashe kofin ba da wuya a biya su basussukan da suke bi.
Sannan an ruwaito Hukumar NFF din ta biya ’yan kwallon alawus din Dala 100 a kullum har na tsawon kwana 10 da suka shafe a kasar Gambiya suna samun horo kafin su wuce Senegal inda shi ma ya kai kwatankwacin Dala dubu 1 wanda ya yi daidai da Naira dubu 251.
kungiyar kwallon kafa ta U-23 dai ta lashe kofin ne bayan ta lallasa Aljeriya da ci 2-1.  Yanzu kungiyar da kasar Aljeriya da kuma Afirka ta Kudu ne suka haye zuwa  gasar Olamfik da za a yi a badi a kasar Brazil.