✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NFF ta ci tarar Samson Siasia Naira dubu 500

Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) ta ci tarar kocin kungiyar kwallon kafa na ’yan kasa da shekara 23 (U-23) Samson Siasia tarar Naira dubu…

Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) ta ci tarar kocin kungiyar kwallon kafa na ’yan kasa da shekara 23 (U-23) Samson Siasia tarar Naira dubu 500 bayan ta aika masa da takardar gargadi.

Hukumar ta ce ta yi haka ne a kan kalaman da kocin ya yi wa kafafen watsa labarai wadanda ba su yi wa hukumar dadi ba.
Shi dai Siasia a makon jiya ne aka ji yana fadin hukumar NFF ba ta biya shi albashin watanni uku ba, sannan kuma kimanin watannin tara kenan ba ta biya ’yan kwallonsa wadansu alawus-alawus da suke bin ta bashi ba, al’amarin da zai iya shafar kokarin da kungiyar ke yi na naman hayewa gasar Olamfik da zai gudana a Brazil a shekara mai zuwa.
Kocin ya bayyana takaicinsa ganin a watan nan ne kungiyar za ta tafi Senegal don fafatawa a gasar cin kofin Afirka na matasa na ’yan kasa da shekara 23 (U-23). Kuma kasashen da suka samu nasara a gasar ce za su haye zuwa gasar Olamfik da zai gudana a badi a kasar Brazil.
Aminiya ta kalato a makon jiya cewa kocin ya nuna kada wanda ya zarge shi idan kungiyar ta kasa tabuka abin a-zo-a-gani a Senegal saboda yadda Hukumar NFF ta yi biris da su. Hakan ce ta sa wadansu daga cikin ’yan wasan da ya gayyato suka nuna halin ko-in-kula na halartar sansanin horar da su a kan lokaci.
Sai dai NFF ta ce abin da ya bata mata rai shi ne yadda ta yi wa kococin kungiyar kwallon kafa na kasar nan kama tun daga kan Sunday Oliseh zuwa kasa bayanin halin rashin kudin da ta tsinci kanta a ciki, kuma Siasia na cikin wadanda suka halarci taron. Amma abin mamaki sai ga shi ya fito duniya yana zargin hukumar da rashin biyansa albashin watanni uku ba tare da neman izinin hukumar ba.
Tuni dai NFF ta aikawa Siasia takardar tuhuma (kuery) inda daga bisani kuma ta aika masa da takardar gargadi (warning) akan idan ya sake aikata haka za ta dauki mataki a kansa. Hakan ya sa ta ci tararsa Naira dubu 500 a bisa laifin da ya yi.
Wani rahoto da ya fito daga NFF ya nuna tuni aka umarci mataimakin kocin Super Eagles Salisu Yusuf ya zauna a shirin ko ta kwana na tafiya da kungiyar U-23 zuwa Senegal.
Najeriya za ta kara ne da kasashen Egypt da Mali da kuma Aljeriya a gasar da za a fara daga ranar 28 ga watan nan da muke ciki a Senegal a gasar cin kofin Afirka na matasa inda daga nan ne za a tantance kasashen da za su wakilci Nahiyar Afirka a gasar Olamfik.