Rahotannin da ke fitowa daga Sifen sun nuna wani Alkali ya umarci shahararren dan kwallon FC Barcelona Neymar da ya gurbana a kotu a ranar 2 ga watan gobe a kan zargin da ake masa na rashin biyan cikakken haraji a lokacin da ya canza sheka daga kolub din Santos na Brazil zuwa na FC Barcelona da ke Sifen a shekarar 2013.
Hukumar kula da kwallo ta Sifen (FA) dai ta zargi dan kwallon da dillalinsa da kuma mahukunta kulob din Barcelona a kan rashin biyan cikakken haraji a shekarar 2013 a lokacin da dan kwallon ya koma kulob din Barcelona.
Alkali Jose de la Mata ya umarci Neymar da ya kasance a gaban kotunsa a ranar 2 ga watan gobe don ya kare kansa. Haka kuma alkalin ya nemi shugaban kulob din Barcelona Josep Maria Bartomeu da shi ma ya hallara a kotu don ya bayar da bayanin yadda al’amarin ya kasance. Sai dai shugaban zai bayyana ne kwana daya kafin Neymar ya halarci zaman kotun.
Haka kuma kotun ta bukaci tsohon shugaban kulob din Barcelona Sandro Rosell da shi ma ya halarci zaman kotun a bisa wannan dambarwa.
Idan za a tuna, tsohon shugaban ya yi murabus ne jim kadan bayan Hukumar shirya kwallon kafa ta Sifen (FA) ta bankado almundahanar rashin biyan cikakken harajin da aka kayyade a cinikin Neymar al’amarin da ta sa ya yi murabus a wancan lokaci.
A wannan karon kotu za ta cigaba da shari’ar ce don gano gaskiyar lamari, kuma akwai yiwuwar a hukunta dan kwallon da kulob din Barcelona muddin aka same su da laifi.
Neymar zai gurfana a gaban Alkali
Rahotannin da ke fitowa daga Sifen sun nuna wani Alkali ya umarci shahararren dan kwallon FC Barcelona Neymar da ya gurbana a kotu a ranar…