Neymar ya karya tahirin Pele na yawan cin kwallo a Brazil, bayan ɗan wasan ya ci kwallo biyu a wasan da suka yi nasara kan Bolivia.
Dan wasan mai shekara 31 wanda ya je wasan share fagen Gasar Kofin Duniya da kwallo 77, ya kuma zubar da bugun fenariti gabanin ya ci kwallo biyu a wasansa na 125 da ya doka wa tawagar ƙasar.
“Ban taba kawo wa zan iya haɗa wannan tarihi ba. Ban fi Pele ba ko wani ɗan wasa a tawagar Brazil ba,” in ji Neymar.
Pele, wanda ya rasu a watan Disamba yana da shekara 82, ya ci wa Brazil kwallo 77 a wasanni 92 da ya buga wa kasar daga 1957 zuwa 1971.
Ana masa kallon ɗaya daga cikin ’yan kwallon da ba a taɓa yin irinsu ba a fagen sana’ar ƙwallon kafa a duniya.
A bayan nan ne dai Neymar wanda tsohon dan wasan Barcelona ne ya bar Paris Saint-Germain zuwa kungiyar Al Hilal ta kasar Saudiyya.