Hukumar Kididdigar Kasar Peru ta bayyana cewar a yayin da duniya ke alhinin rasa Pele, gwarzon dan kwallon kafa na karni, sunansa zai rayu a tsakanin yara fiye da 700 ‘yan kasar da aka haifa a karshen shekarar 2022.
Jerin sunayen da jami’an kasar ta Peru suka fitar ya nuna cewar, bayan mutuwarsa gwarzon dan kwallon kafar, an rada wa jarirai 738 da aka yi wa rajista a hukumance sunan ko dai Pele, ko King Pele, ko kuma Edson Arantes ko Edson Arantes do Nascimento, cikakken sunan zakaran kwallon kafa na duniya sau uku.
- A karshen watan Yuni za mu dakatar da biyan tallafin man fetur —Ministar Kudi
- Mutum 18 sun kone kurmus a hatsarin mota a Bauchi
A ranar 29 ga watan Disamba Pele ya mutu yana da shekaru 82 a duniya, wanda kuma aka binne shi a ranar Talata.
Iyayen yara a kasar Peru dai sun saba rada wa ‘ya’yansu sunayen fitattun mutane da suke kauna walau a cikin ‘yan wasa ko kuma shugabanni kamar yadda RFI ya ruwaito.
Wata kididdiga ta nuna cewar a yanzu haka, sunan Cristiano Ronaldo ne aka fi rada wa yaran kasar, wadanda adadinsu ya kai dubu 31 da 538.
Messi kuwa na da takwarori jarirai 371 ne a baya bayan nan a kasar ta Peru, wadanda ko dai aka sanya musu suna Leo Messi, ko Messi kadai bayan da ya lashe Gasar Kofin Duniya.