✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gagarabadau: An sanya sunan Pelé a Kamus

Pele dai ya mutu a watan Disamban bara yana da shekara 82.

Lakabi Pelé, da ake fada wa marigayi gwarzon dan kwallon duniya, bisa ka’ida ya shiga cikin kamus, inda yake nufin “zakakuri ko fintinkau ko abu na daban.”

Ƙamusun harshen Fotugal (Portuguese) mai suna Michaelis, daya daga cikin mafi shahara a Brazil, ya sa sunan “pelé” a matsayin sabuwar kalmar siffa a kundinsa na intanet.

Sanya sunan a cikin Kamus din ya zo ne bayan wani gangami da Gidauniyar Pele ta kaddamar na neman a karrama tauraron dan kwallon, inda ya samu amincewa har mutane fiye da 125,000 suka sa hannu.

Pele dai ya mutu a watan Disamban bara yana da shekara 82.

Shi kadai ne dan kwallon da ya ci Kofin Duniya sau uku, kuma mutane da yawa na daukar sa a matsayin dan kwallon kafa mafi fice a tarihi.

A lokacin sana’arsa ta kwallon kafa tsawon shekara 20, ya ci kwallayen masu yawa a tarihi har 1,281 lokacin da ya buga wa kungiyar Santos ta Brazil da kuma a kasar Brazil da kulob din Cosmos na New York.

Tun rasuwarsa, sanadin larurorin da ya yi fama da su na cutar dajin hanji, tsohon kulob dinsa Santos da tashar wasanni ta Sport TV da Gidauniyar Pelé suka yi ta matsa lamba don ganin an martaba sunan tauraron kwallon kafar na duniya, ta hanyar shigar da shi cikin Kamus.

A ranar Laraba ne kuma, masu buga Kamusun Michaelis suka sanar da cewa za a shigar da kalmar cikin kundin kalmominsu na intanet a nan take.

Kuma da zarar an zo wallafa kwafen takarda na kamus Michaelis nan gaba za a hada da kalmar pele.

An sanya sunan kamar haka: “pe.lé adj. (siffa) Mutum wanda ya zarce saura, wanda nagartarsa, kima ko fifikonsa ba daya ne da komai ko da kowa ba, kamar dai Pelé, laƙabin Edson Arantes do Nascimento (1940-2022), wanda ake dauka a matsayin dan wasa mafi gawurta a tsawon dukkan zamani kuma zakakuri, mai fintinkau kuma na-daban.”

Gidauniyar Pelé, wadda kungiyar agaji ce da aka kafa don alkinta tarihin gwarzon dan kwallon, ta ce karramawa ce da ta dace ga “Sarki”.

“Kalmar da tuni ake amfani da ita wajen bayyana mutumin da ya yi fice kan abin da yake yi, ta shiga shafukan kamus!,” ta wallafa a sakon Twitter.

BBC