Dan wasan kwallon kafan kasar Brazil da kuma kungiyar Paris Saint-German, Neymar da Silva Santos Junior ya raba gari da kamfanin kayan wasa na Nike da ke daukar nauyinsa.
Nike na kasar Amurka ya sanar da daina daukar nauyin Nyemar, lamarin da ya kawo karhsen daya daga cikin yarjejeniya mafiya tsada da kamfanin ya kulla na daukar nauyin dan wasan tun yada da shekara 13.
Mai Magana da Yawun Nike, Josh Benedek ya ce, “Ina tabbatar maka cewa yanzu Neymar ba dan wasan Nike ba ne”, sai dai bai yi karin bayani ba.
Diario do Peixe ta ce a ranar Talata dan wasan na PSG zai bar Nike da ya dauki nauyinshi tun kafin ya zama kwararren dan wasa. Neymar bai fita a cikin tallan Nike ba.
Wasu rahotanni na cewa Neymar ya fara tattaunawa da kishiyar Nike, wato kamfanin Puma na kasar Jamus domin daukar nauyinsa.
Matakin Neymar na iya barazana ga Nike da PSG
PSG na iya fuskantar barazana sakamakon rabuwar Neyar da Nike, wanda a tsawon lokacin da yake tare da Nike, kungiyar kan samu kayan wasa kyauta daga kamfanin.
Bayan da Neymar ya dawo PSG bayan barinsa Barcelona, Nike ka ba PSG Yuro miliyan 70 a duk shekara. Rabuwar dan wasan da Nike zai ja mata asarar wadannan kudade.
Tafiyar dan wasan na Brazil zai yi illa aga Nike mai tallata kayansa ta hanyar daukar nauyin kungiyoyi da ’yan wasa a manyan birane duniya kamarsu: New York, London, Shanghai, Beijing, Los Angeles, Tokyo, Paris, Berlin, Mexico City, Seoul da Milan.
A gefe guda kuma, a cikin kasa shekara biyu Puma ta kutsa wajen tallata sunayensa a kungyoyin wasa inda ya kashe Yuro miliyan 700, kuma da alama ba a nan zai tsaya ba.
Neymar da Puma na iya daidatawa
Puma na kokarin kammala kulla yarjejeniya kwantaragi da kungiyoyin Manchester City, PSV Eindhoven, AC Milan, Valencia FC da kuma sabunta kwangilarta da kungiyar Borussia Dortmund na kasar Jamus.
Sannan ta shiga jerin kamfanonin da ke daukar nauyin gasar LaLiga a kasar Spain, inda a jikin kwallon akwai zanen tambarin Puma.
Kamfanin na ta kara kaimi wajen kara daukar hankali a wannan kakar kuma ya dage wajen ganin daidaita da Neymar.