✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Netanyahu ya amince da sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Isra’ila ta hakikance cewar akwai sauran kimanin mutane 130 da ake garkuwa da su a Gaza

Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu ya amince da sabuwar tattaunawa domin kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

Sabuwar tattaunawa dai za ta gudana a biranen Doha da Alqahira, a cewar sanarwar da ofishinsa Netanyahu ya fitar a ranar Juma’a.

Tun bayan da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya zartar da ƙudirin neman a gaggauta tsagaita wuta a Gaza a Litinin ɗin da ta gabata, Isra’ila da kungiyar Hamas ke zargin juna da gazawa wajen cimma yarjejeniyar.

A Talatar da ta gabata, mai shiga tsakani kasar Qatar ta ce ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Hamas da Isra’ila kan tsagaita wuta a Gaza tare da sakin mutanen da ake garkuwa da su.

Sai dai dukkanin bangarorin da ke rikici da juna da mai shiga tsakanin ba su yi karin haske game da lamarin ba.

Ofishin Netanyahu ya ce firaministan ya zanta da shugaban hukumar leken asirin Isra’ila, Mossad David Damea game da tattaunawar sulhun.

Sai dai ba a bayyana ko Damea ɗin zai yi balaguro zuwa biranen Doha da Alqahira domin halartar tattaunawar ba.

Yaƙi ya barke tun bayan da Hamas ta kaddamar da wani hari da ba a taba ganin irinsa ba, wanda ya yi sanadiyar asarar rayuka 1,160, galibinsu farar hula, a cewar kididdugar gwamnatin Isra’ila da Kamfanin Dillancin Labaran AFP ya ruwaito.

A cewar ma’aikatar lafiya da ke karkashin gudanarwar kungiyar Hamas, Isra’ila ta ƙaddamar da harin ramuwar gayyar a kan Hamas wanda ya yi sanadiyar asarar rayuka mazauna yankin Gaza dubu 32 da 623 galibinsu mata da kananan yara.

Falasɗinawa masu fafutuka da makamai sun yi garkuwa da Yahudawa da baki ’yan kasashen ketare 250 a yayin harin da aka kai wa Isra’ila na ranar 7 ga watan Oktoban bara, sai dai an saki da dama yayin tsagaita wutar mako guda da aka yi a watan Nuwambar na barar.

Isra’ila ta hakikance cewar akwai sauran kimanin mutane 130 da ake garkuwa da su a Gaza, ciki har da mutum 33 da ake zaton sun mutu; sojoji 8 da farar hula 25.