Wani rahoton shirin binciken kwakwaf na ‘BBC Africa Eye’ ya gano yadda wasu masu magani ke damfarar mutane masu da sunan bayar da maganin coronavirus.
Binciken ya bankado yadda ’yan damfarar a Najeriya da Ghana ke yi wa jama’a romon baka, da kuma hadarin da magungunan ke da shi ga rayuwar dan Adam.
Hukumar Kula da Magunguna ta Ghana (FDA) ta gano cewa daya daga cikin magungunan “na dauke da Ecoli wanda ake samunsa a cikin bayan gida da dattin ciki”, inji Anas Aremeyaw Anas, dan jaridar da ya yi binciken kwakwaf din.
‘BBC Africa Eye’ ya mayar da hankali a kan maganin cutar coronavirus ne, lura da cewa miyagu kan yi amfani da matsalar, wadda ta addabi al’umma, a matsayin damarsu ta cutar mutane da samun kudi.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce har yanzu babu magananin cutar coronaviru wadda bullarta ta karkatar da hankalin cibiyoyin bincike da kamfanonin harhada magunguna zuwa kokarin nemo magani da kayan jinyar masu ita a fadin duniya.
Hakan ta sa Anas yin shigar burtu a matsayin wanda dan uwansa ke fama da COVID-19 domin fallasa masu damfarar da ke sayar wa mutane maganin cutar na karya.
Rahoton na Anas ya haifar da tattaunawa ya kuma farkar da jama’a da ma hukumomi su fara daukar mataki a kan matsalar.
Ga abubuwan da binciken ya gano, kamar yadda ya bayyana a takaice a wata hira da BBC ta yi da shi ta waya.
‘Maganin COVID-19 a Najeriya’
Binciken ya gano wasu masana kimiyya da masu maganin gargajiya da ma malaman addini ke riya cewa suna da maganin cutar suna kuma warkar da masu ita.
“Misali akwai Dakta Abodo, wanda masanin kimiyyar harhada magunguna ne, da ke da’awar cewa yana da maganin coronavirus da kuma cutar HIV/Aids.
“Bayan shi akwai wani mai maganin gargajiya da wani fasto wadanda ko wannensu ke ikirarin cewa yana da maganin cutar”, inji Anas.
Duk da cewa ba a kai magungunan an yi gwaje-gwaje domin tabbatar da ingancinsu ba, “sanin kowa ne WHO ta riga ta shelanta cewa har yanzu cutar HIV da COVID-19 ba su da magani tukuna.
“Saboda haka a matsayinmu na ’yan jarida, idan mutum ya ce yana da maganinsu, dole mu sa masa alamar tambaya”, inji shi.
Ghana: Abdellah Brothers da COA FS
Binciken ya gano wasu kamfanoni biyu da ke cewa suna da maganin cutar suna kuma sayar wa mutane a Ghana.
Misali, kamfanin COA FS ya wallafa a shafinsa na intanet karara cewa COVID-19 ba ta da magani.
“Amma da na je ofishinsu sai na iske ba wai sayar da maganin cutar kadai ba, za ma su rubuta mini yadda zan yi amfani da shi har in warke daga cutar”, a cewarshi.
Su kuma Abdella Brothers har tallatawa suke yi a kafafen yada labarai cewa suna warkar da cutar.
“Sukan sanya sharadi, cewa ba za a iya sayan maganin kai tsaye daga wurinsu ba, sai ta hannun wakilansu.
“Amma da muka yi shigar burtu muka je ofishinsu sai muka tarar suna ta sayar da maganin”.
Sun kuma yi wa maganin nasu mai suna “Covid Cure” tambarin inganci na FDA na jabu.
Kamfanin ya yi ikirarin cewa ya warkar da wasu mutane da kananan yara da suka kamu.
Sun kuma yi yunkurin sayar wa ’yan jaridar kwalabe 100 na maganin nasu a kan Cedi 150,000 (kimanin Dalar Amurka 26,000).
Amma da FDA ta gudanar da gwaji a kan maganin, sai ta gano cewa gaba dayansa gurbataccen abu ne mai dauke da Phosphine, wanda ke da matukar hadari ga rayuwa.
“Da ma idan mutane idonsu ya rufe suna neman kudi, za ka ji suna fadar abubuwan da suka saba hankali.
“Alal misali, suna cewa su suka warkar da Mataimakin Shugaban Kasar Senegal daga cutar, alhali babu mataimakin shugaban kasa a Senegal.
“Suna kuma cewa Sarkin yankin Asanti ya kulla yarjejeniyar fiye da Dala 150,000 [da su].
“Suna fadar wadannan abubuwan ne domin mutane su yarda, kuma mutane na yarda sun kuma sayi maganin”, inji dan jaridar.
Ingancin magungunan
Domin gano gaskiya, akwai bukatar samun hujja ta kimiyya game da ikirarin da kamfanonin magungunan suka yi, kafin a yarda ko a yi watsi da ikirarin nasu.
Dan jaridar ya gabatar da samfurin magungunan ga Hukumar FDA domin tabbtar da ingancinsu.
“Sakamakon gwajin mai matukar tayar da hankali ne, cewa guba ce mai hadarin gaske ga rayuwar dan Adam, don haka bai dace mutum ya sha ba”.
Gwajin ya kuma gano cewa “akwai phosphine a cikin maganin, wanda ke da hadarin gaske, zai kuma iya haddasa matsaloli, da sauran sunadarai masu hadari ga dan Adam”.
Tuni Hukukumar ta FDA ta yi karar kamfanonin ta kuma gurfanar da jami’ansa guda biyu.
Tun kafin binciken Anas, FDA ta gano maganin COA FS na dauke da sinadarin Ecoli, wanda ake samu a cikin bayan gida.
Girman matsalar a Afirka
Binciken ya kuma gano yadda matsalar ta damfarar mutane da sunan maganin cutar ta yadu a kasashen Afirka.
“Bayan bidiyon da na yi, abokan aiki daga sassan Afirka sun yi ta cewa ‘ka farkar da mu saboda mun sha ganin masu kokarin tatsar mutane ta wannan hanya’.
“Kar ka manta cewa ana sayar da wadannan magunguna ne da tsada sosai, kuma da gaske suke yi.
“Misali, kudin na Abdalleh Brothers wanda suka so su sayar min da kwalabe 100 ya haura Dalar Amurka 25,000”.
Masu irin wannan sana’a kan yi amfani da rashin maganin wannan cuta ne wajen tatsar jama’a ta hanyar ikirarin cewa magungunan nasu na warkarwa kuma kariya ne daga cutar.
“Saboda haka idan kana da dan uwa da ya kamu da COVID-19 ga shi babu magani, ba ka da zabi face ka jarraba nasu”.
Matsalar likitocin bogi a Afirka
Abin da binciken ya bankado shi ne hadarin yawaitar likitocin bogi a nahiyar Afirka ya fi na cutar coronavirus.
“Mu tuna, akalla mutum 100,000 ne ke mutuwa a duk shekara a hannun likitocin bogi a duniya, wadanda dubu talatin daga cikinsu ke mutuwa a Afirka.
“Ayyukansu sun kashe mutane fiye da wadanda coronavirus ta kashe, kuma har yanzu ba dainawa suka yi ba”.
Mene ne abun yi?
“Hakki ne a kan ’yan jarida da kungiyoyi su sa ido a kan ayyukan wadannan miyagu, su rika wayar da kan jama’a akai-akai.
“Zura wa hukumomi ido su magance kowacce matsala ba zai wadatar ba, domin wani lokaci abin kan yi musu yawa.
“Aikin kowannenmu ne fahimtar da al’umma cewa ko da yake maganin gargajiya na da amfani, kar a sake mu sha wani abu sai an tabbatar da ingancinsa da irin tasirin da zai yi a jiki.
“Matsalar ta yadu, saboda tana bukatar kowa a cikinmu ya bayar a gudunmuwa a yake ta”, inji Anas.
Me hukumomi suke yi a kai?
“Ina gani FDA ta riga ta dauki mataki, amma aikinmu ne gaba daya ba na gwamnati kadai ba, domin mu ne ke amfani da wadannan kayayyaki.
“Mu farka, sannan mu sanar da kungiyoyi duk abin da muka gani domin mu san matakin da ya kamata a dauka”, inji Anas.
Nagartar hukumomi
Ba za a yi wa hukumomin kula da magunguna a kasashen Afirka kudin goro ba game da yadda suke aikin yakar wannan matsala.
“Amma na san FDA na fama da matsalar karancin ma’aikata da rashin isassun kudade da sauransu, kamar dai sauran hukumomin gwamnati.
“Haka ake fama da irin wadannan matsaloli a kasashen Saliyo da Kenya da Afirka ta Kudu.
“Saboda haka dole mu da ke zaune a cikin al’ummomi ne za mu taimaki kanmu da kanmu, kar mu zaci cewa wani ne zai zo ya yi mana abin da ya kamata”, inji shi.
Abin da ke sa mutane karbar magungunan
“Na farko akwai karancin ilimi a nahiyar Afirka, musamman a yankunan karkara.
“Saboda haka akwai gagarumin aiki a gaban ma’aikatun yada labarai na su tashi haikan su wayar da kan jama’a cewa su guji shan abin da zai iya yin barazana ga lafiyarsu da sunan magani.
“Ko da yake za a iya dadewa kafin cimma bukata, nauyi ne a kanmu a matsayinmu na ’yan jarida da malaman addini da sauransu mu yi amfani da duk damar da muka samu mu rika wayar da kan al’ummomi cewa su guji shan kowane irin tarkace da sunan magani”.
COA FS na ikirarin cewa sun warkar da masu cutar a kasar China.
Sai dai har yanzu ba a ji hukumomi ko wani dan kasar da ya ce ya warke ta dalilin amfani da maganin kamfanin ba.
“Abin alfaharin Ghana ne a ce COA FS na da maganin, amma dole mu fadi gaskiya.
“A halin yanzu, maganin nasu bai dace ga dan Adam ya yi amfani da shi ba”, inji Anas.