More Podcasts
Farashin magunguna a asibiti na ci gaba da tashin gwauron zabo a Najeriya, lamarin da ke jefa marasa lafiya da ’yan uwansu cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi.
A sakamakon haka, marasa lafiya da dama sukan koma amfani da abin da ya fi musu sauki — ko dai sayen maganin a hannun masu tallan sa a kafaɗa, ko amfani da maganin gargajiya, ko kuma, a wasu lokutan, su haƙura da maganin ɗungurungum.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ake Hana ’Yan Najeriya Fadin Albarkacin Bakinsu
- DAGA LARABA: Abin ya sa ’yan Nijeriya ke kishin ƙabila fiye da ƙasa
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan halin da marasa lafiya suka shiga a sakamakon tashin gwauron zabo da maganin asibiti ya yi.
Domin sauke shirin, latsa nan