✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Neman Buhari ya yi murabus ba zai magance matsalar tsaro ba —Fadar Shugaban Kasa

A sani wannan matsala ce fa da ta dade shekara da shekaru ana fama da ita.

Fadar Shugaban Kasa ta yi martani kan kiraye-kirayen neman Shugaba Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki saboda gaza magance matsalar tsaron da kasar nan ke fuskanta da ya yi.

A Yammacin Talatar da ta gabata ce Kungiyar Dattawan Arewa ta bakin mai magana da yawunta, Dokta Hakeem Baba-Ahmed ta nemi shugaba Buhari ya yi murabus.

A martanin da mai magana da yawun Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba, ya ce Fadar Shugaban Kasa tana kan fito da wani gagarumin tsarin tsaurara tsaro a fadin ƙasar nan, nan ba da dadewa ba.

Shehu ya ce murabus din shugaban ƙasa ba shi ne mafita ba ga matsalar tsaron da ake fama da ita.

Ya ce tuni jami’an tsaro sun kara kaimi wajen dakile ‘yan ta’adda, musamman a Jihar Kaduna da Neja da kuma yankin Neja Delta, kamar dai yadda Shugaban Kasa ya umarce su.

Garba ya ce bangarorin tsaro sun hada kai wajen ci gaba da farmakin yin galaba a kan masu haddasa matsalar tsaro, kuma ana ganin alamun nasara.

“Fadar Shugaban Kasa ba ta so ta na biye wa masu neman jan ta ana hauragiyar cika kafafen yada labarai da maganganu, kamar yadda Kungiyar Dattawan Arewa ta yi.

“Son neman a sani aiki ne na ‘yan siyasar da suka kasa samun yardar talakawa masu zabe.

“Ya isa ta bangaren mu, mu fito mu ce murabus din Shugaban Kasa a yanzu ba shi ne mafita daga matsalar tsaron da kasar nan ke fuskanta ba.

“A sani wannan matsala ce fa da ta dade shekara da shekaru ana fama da ita, daga nan kuma wannan gwamnatin ta gaje ta, bayan gwamnatocin baya sun yi watsi da kokarin dakile ta.

“Yana da muhimmanci kwarai jama’a su san irin kokarin da wannan gwamnatin ke yi, wajen ganin ta magance matsalar tsaro.

“Su kuma ‘yan siyasa yana da kyau su sani kamata ya yi su taimaka kasa ta dore, ta yadda idan lokacinsu ya yi, su ma su sami wurin da za su yi wa mulki.

“Saboda idon mutum idanunsa suka rufe wajen neman mulki, bai kamata ya tarwatsa kasar da ya ke son ya dare kan mulkinta ba.

“Ma’aikatar Tsaro na bakin kokarinta wajen ganin cikin gaggawa kwanan nan ta fito da tsare-tsare da kuma kai farmaki a yankunan Kaduna da Neja, kamar yadda Shugaba Kasa ya ba su umarni.

“A wurin Taron Majalisar Zartaswa na ranar Laraba, an amince a sayo tulin makaman da ba a taba kawo masu yawansu ba a lokaci guda.”

Ya kara da cewa, Gwamnatin Tarayya za ta cika alkawarinta na samar da dawwamammen zaman lafiya a fadin Najeriya.