Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ta sake karbar wasu ‘yan Najeriya su 117 da aka dawo da su daga kasar Libya.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata a Legas.
- Qatar 2022: Zargin tauye hakkokin baki ya dabaibaye Qatar
- An gano wata masana’antar wayoyin iPhone na jabu
NEMA ta ce wadanda suka dawo sun isa filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Ikeja a Jihar Legas a cikin jirgin Al Buraq Air Boeing 737-800 da misalin karfe 4.20 na yammacin Talata.
NEMA ta ce wadanda aka dawo da su din sun hada da maza 90, mata 23 da jarirai hudu wadanda Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM) ta taimaka wajen dawo da su gida Najeriya.
Jakadancin Najeriya a Libya, Ambasada Kabiru Musa, a wata sanarwa da ya fitar ya sanar da kwashe mutanen zuwa Najeriya.
Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya bai wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), a ranar Talata a Abuja.
Musa ya ce gwamnatin Najeriya ta hada kai da IOM wajen kwashe mutanen.
Musa ya ce daga cikin karin mutanen 117 da aka kwashe sun hada da mutane 48 da aka sako daga wuraren da ake tsare su a Libya.
“Gwamnatin Tarayya ta dukufa wajen ganin cewa babu wani dan Najeriya da ta bari a makale a kasar waje.
“Burin Najeriya a Tripoli shi ne ta ci gaba da yin aiki tare da hukumomin Libya don tabbatar da cewa babu wani dan kasarmu da ke tsare ba bisa ka’ida ba, kuma za ta tabbatar da mayar da su gida.”
Ya ce ma’aikata daga hukumomin da abin ya shafa za su kasance a kasa domin karbar mutanen da suka isa Legas.