Hukumar Agaji ta Kasa (NEMA) ta karbi ’yan Najeriya 105 da suka makale a kasar Chadi.
Kodinetan hukumar a Jihar Kano, Dokta Nuradeen Abdullahi ne, ya ce an dawo da su Kano ne karkashin kulawar Hukumar Musu Gudun Hijira ta Duniya (IOM), ta hanyar shirin mayar da kasashensu.
- Bukatu 6 da muka mika wa Buhari —Sheikh Daurawa
- DAGA LARABA: Yadda Talla Ke Bata Rayuwar Yaran Arewa
Da yake karbar su a a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano, jami’in ya ce, “An dawo ’yan Najeriya ne da suka bar kasar nan don neman abun dogaro da kai a kasashen Turai, amma suka kasa dawowa gida.
“Mutanen sun hada da maza 24, mata 23 da yara 58 kuma sun fito ne daga jihohin Katsina, Kano, Adamawa, Borno, Yobe da Taraba da sauransu,” in ji shi.
Abdullahi ya bayyana cewa za a horar da su na tsawon kwanaki hudu a kan sana’o’in hannu, kuma za a ba su tallafi don dogaro da kai, inda ya bukace su da su zama masu koyi da kyawawan halaye.
Ya kara da cewa daga watan Mayu zuwa Oktoban 2022, hukumarsa ta karbi ’yan Najeriya 560 da suka makale daga Jamhuriyar Nijar da Sudan.
Daya daga cikin wadanda suka dawo, Aminu Musa, ya ce ya je kasar Libya ne domin neman aikin yi saboda shi maraya ne kuma mahaifiyarsa ba ta da lafiya.
“Mun shiga tsaka mai wuya, don haka na yanke shawarar neman mafita.
“A zaman da na yi a Libya na tsawon shekara biyu, an sace abokina da muka tafi tare da shi.
“Mun sha wahala sosai, daga karshe na yanke shawarar komawa Chadi saboda tsoron kada a sace ni. Ikon Allah ne kadai ya sa na dawo gida,” in ji shi.