✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NECO ta sa ranar jarabawar daliban da hargitsin EndSARS ya hana su rubutawa

Dalibai 233,000 za su yi jarabawar da zanga-zangar EndSARS ta hana rubutawa

Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa (NECO), ta ce dalibai 233,000 da tarzomar zanga-zangar EndSARS ta hana su rubuta jarabawarta ta 2020 za su rubuta jararbawarsu daga watan Fabrairun 2021.

Shugaban NECO, Farfesa Godswill Obioma, ya ce Hukumar ta samar wa daliban damar yin jarabawar a lokacin jarabawar dalibai masu zaman kansu daga ranar Litinin 1 ga watan Fabrairu zuwa Laraba 3 ga watan Maris, 2021.

Farfesa Godswill Obioma ya bayyana haka ne a lokacin da ya sanar da fitar da sakamakon jarabawar NECO ta kammala sakandare (SSCE) ta 2020 ranar Laraba a Minnna, Jihar Neja.

Ya ce jihohin da tarzomar zanga-zangar EndSARS ta hana gudanar da jarabar daliban makarantu su ne: Kano, Abuja, Legas, Ogun, Oyo, Abia, Inugu, Edo, Ribas, Ondo, Ekiti, da kuma Osun.

Darussan da tarzomar ta kawo wa cikas su ne:  ‘Chemistry practical, Economics, Technical Drawing, Food and Nutrition, Further Mathematics’.

Ya yi bayanin cewa NECO za ta jinkirta fitar da sakamakon daliban na darussan da hakan ta shafa sai daga baya idan sakamakon jarabawar da za su rubuta ta fito.

“Daliban ba za kara biyan ko sisi ba.  Idan aka fitar da sakamakon jarabawar daliban makarantu na 2020, ba za a bayyana na daliban da matsalar ta shafa a wadannan darussan ba sai daga baya idan sun rubuta kuma sakamako ya fito,” inji shi.

Dalibai 1,221,447, suka yi rajistar rubuta jararbawar NECO (SSCE) a fadin Najeriya, wadan daga cikinsu mutum and 1,209,992, suka rubuta.