Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa (NECO), ta ce dalibai 233,000 da tarzomar zanga-zangar EndSARS ta hana su rubuta jarabawarta ta 2020 za su rubuta jararbawarsu daga watan Fabrairun 2021.
Shugaban NECO, Farfesa Godswill Obioma, ya ce Hukumar ta samar wa daliban damar yin jarabawar a lokacin jarabawar dalibai masu zaman kansu daga ranar Litinin 1 ga watan Fabrairu zuwa Laraba 3 ga watan Maris, 2021.
- Tashar Buhari: Da N30 sai a kai ka har gida a Kano
- Yadda za ku duba sakamakon jarabawar NECO 2020 cikin sauki
- Nuna tsiraici: Bidiyon sabuwar wakar Hausa ya ta da kura a intanet
- Tsadar hatsi na neman fin karfin mutane a Kaduna
Farfesa Godswill Obioma ya bayyana haka ne a lokacin da ya sanar da fitar da sakamakon jarabawar NECO ta kammala sakandare (SSCE) ta 2020 ranar Laraba a Minnna, Jihar Neja.
Ya ce jihohin da tarzomar zanga-zangar EndSARS ta hana gudanar da jarabar daliban makarantu su ne: Kano, Abuja, Legas, Ogun, Oyo, Abia, Inugu, Edo, Ribas, Ondo, Ekiti, da kuma Osun.
Darussan da tarzomar ta kawo wa cikas su ne: ‘Chemistry practical, Economics, Technical Drawing, Food and Nutrition, Further Mathematics’.
Ya yi bayanin cewa NECO za ta jinkirta fitar da sakamakon daliban na darussan da hakan ta shafa sai daga baya idan sakamakon jarabawar da za su rubuta ta fito.
“Daliban ba za kara biyan ko sisi ba. Idan aka fitar da sakamakon jarabawar daliban makarantu na 2020, ba za a bayyana na daliban da matsalar ta shafa a wadannan darussan ba sai daga baya idan sun rubuta kuma sakamako ya fito,” inji shi.
Dalibai 1,221,447, suka yi rajistar rubuta jararbawar NECO (SSCE) a fadin Najeriya, wadan daga cikinsu mutum and 1,209,992, suka rubuta.