✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar 2024

Jihohin Abiya da Imo da Ebonyi ne kan gaba a samun sakamako mai kyau.

Hukumar Shirya Jarrabawa ta Ƙasa (NECO) ta fitar da sakamakon jarrabawar kammala sakandare ta 2024 (SSCE).

Magatakarda kuma Shugaban Hukumar NECO, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a hedikwatar hukumar da ke birnin Minna na Jihar Neja.

Ya ce adadin dalibai 828,284, wanda ke wakiltar kashi 60.55 cikin 100 ne suka samu nasarar cin darussa biyar da suka haɗa da Ingilishi da Lissafi.

Wushishi ya ce, adadin ɗalibai 1,376,423 da suka hada da maza 709, 950 da mata 669,473 ne suka yi rijistar jarrabawar a shekarar ta bana, yayin da ɗalibai 1,367,736 da suka kunshi maza 702,112 da mata 665,624 ne suka zana jarrabawar.

Shugaban na NECO ya ce adadin waɗanda suka samu nasarar darussa biyar da ko fiye tare da la’akari da darussan Ingilishi da Lissafi ya kai 1,147, 597 da ke zaman kashi 83.90 cikin 100 yayin da adadin masu buƙata ta musamman ya kai 2,267.

Ya ce, akwai adadin ɗalibai 8,437 da ke wakiltar kashi 30.1 cikin 100 na yawan waɗanda suka rubuta jarrabawar da aka same su da maguɗin jarrabawa a wannan shekarar da saɓanin ɗalibai 12,030 da aka samu a shekarar 2023.

Farfesa Wushishi ya bayyana cewa jihohin Abiya da Imo da kuma Ebonyi ne suka kasance kan gaba a samun sakamako mai kyau yayin da jahohin da suka fi faɗuwa sun haɗa da: Katsina da Kano da Jigawa da Borno da kuma Zamfara.

Farfesa Wushishi ya ƙara da cewa, an samu wasu makarantu 40 da suke damfarar jama’a a jihohi 17, inda ya ce za a gayyato makarantun da abin ya shafa domin tattaunawa kafin a sanya musu takunkumi.

Ya kuma ce wata makaranta a Jihar Ekiti an ba da shawarar an tafka maguɗin jarrabawa a cikin manyan darussa biyu masu muhimmanci da kuma ɗaya a fannin kimiyya.