Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa (NECO) ta dage jarabawarta na daliban da sa makaranta (External) da ta shirya fara gudanarwa a ranar Litinin 1 ga watan Fabrairu, 2021.
NECO ta shirya yin jarabawar ne har da daliban makarantu masu kammala sakandare da ba su samu rubuta jarabawarta ta 2020 ba sakamakon rikicin EnSARS a wasu jihohi.
- An bude makarantar ’yan baiwa a Kano
- An cafke dillalan makamai a Jihar Katsina
- ‘Yadda muke shiga kunci yayin zaman zawarci’
- Abubuwa 5 da za su sa budurwa ta so ka
Yanzu an mayar da lokacin fara jarabwar ranar Litinin 8 ga Fabrairu, 2021 sannan a kammala a ranar Laraba 10 ga Maris.
Kakakin Hukumar, Azeez Sani ya ce an dage jarabawar kamar yadda dalibai suka bukata ne domin ba su damar kammala yin rajista.
Ya ce, “Hukumar na sanar da daliban makarantu da ba su samu rubuta jarabawar SSCE na 2020 ba sakamakon tarzomar EndSARS da su lura da sauye-sauyen sannan su halarci cibiyoyin jarabawarsu a sabbin ranakun da aka sanya.”
Sanarwar ta kuma bukaci dalibai masu bukata sabon jadawarin jarabawar da su ziyarci shafin NECO a kan adireshin www.neco.gov.ng