✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ndume ya soki Gwamnonin Kudu kan hana yawon kiwo

Dan Majalisar ya ce gwamnonin sun bar jaki suna dukan taiki kan matsalar tsaro.

Sanata Ali Ndume ya soki gwamnonin Kudancin Najeriya kan haramcin da suka sanya kan yawon kiwo a fadin yankin.

Ndume ya yi caccakar ne bayan matsayin da gwamnonin Kudu suka yi ittifaki a kai a zamansu na ranar Talata, da zummar kawo karshen rikicin manoma da makiyaya.

Amma dan Majalisar Tarayyan ya ce yawon kiwo ba shi ne ya kawo matsalar tsaro a Najeriya ba, amma kowane yankin kasar na da irin matsalar tsaron da ta kebance shi.

“Gwamnonin sun bar jaki suna dukan taiki saboda ba kiwo a waje ba ne matsalar, rashin tsaro ne matsalar, kuma yawancin matsalar tsaron da ke addabar Najeriya ba a daji suke ba.

“Matsalolin tsaron daban-daban hudu ne: Ta’addanci a Arewa-maso Gabas, IPOB  a Kudu-maso-Gabas,  ’yan bindiga a Arewa-maso-Yamma, sai kuma rikicin manoma da makiya a Arewa ta Tsakiya.

“Kudu-maso-Yamma ba ta da wata matsala in banda arangama da aka yi tsakanin manoma da makiyaya da kuma masu karajin kafa kasar Yarabawa.

“Haka a Kudu-maso-Kudu babu matsala, so suke su tunzura Avengers, amma dai yankin na zaune lafiya. Kowane yanki da irin matsalar tsaronsa,” inji Sanatan mai wakiltan Borno ta Kudu.

‘A dakatar da albashi a sayo makamai’

Ndume ya jaddada muhimmancin Shugaba Buhar ya ba da muhimmanci ga sha’anin tsaro, wadata sojoji da makaman yakar ta’addanci yadda ya kamata da kuma biyan albashin sojoji a kan lokaci.

“Ko albashinmu ne ya kama, a dakatar domin samar musu abubuwan da suke bukata, saboda sai da tsaro za a yi maganar wani abu. Ba ’yan siyasa kadai ba, har da kowa.

“Idan mutum ba zai iya fita daga gidansa ba sai ya sallama albashinsa ba zai yi ba? Yawancin mutane daga gida suke aiki ana biyan su. A dakatar da biyan albashi a fara magance matsalar tsaro gaba daya. Idan babu kudi a tsayar da biyan albashi da alawus-alawus a  yi amafi da kudaden wurin samar da tsaro.

“Idan za aka ranci kudi domin samar da gine-gine, to me sai hana ka yi karbi rance domin samar da tsaro ba?” Inji Nduma.

Shugaban Kwamitin Rundunar Sojin Kasa a Majalisar Dattawan ya yaba wa sojoji kan yadda suka dakile harin mayakan Boko Haram da Magaribar ranar Talata a Maiduguri, Jihar Borno.