✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ndume ya jinjina wa Tinubu kan bai wa ’yan Arewa sabbin muƙamai

Ndume ya ce yana da kyau shugaba ya kasance mai sauraren koken jama'a.

Sanata Ali Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, bisa bai wa ’yan Arewa mutum 12 manyan muƙamai a hukumomin gwamnati.

Ya ce wannan matakin ya gyara rashin daidaito da ake gani a naɗin muƙaman da shugaban ya yi a baya, wanda ya janyo damuwa a yankin Arewa.

A ranar Juma’a ne Shugaba Tinubu, ya sanar da sunayen wasu ’yan Arewa da aka naɗa shugabanni a hukumomi kamar su Hukumar Inshorar Noma ta Ƙasa (NAIC), Shirin Tallafa wa Masu Ƙaramin Ƙarfi na GEEP, da Hukumar Inshorar Ma’aikata (NSITF), da wasu cibiyoyin gwamnati.

Ndume ya ce waɗannan muƙamia sun nuna cewa Tinubu na ƙoƙarin gudanar da mulki cikin adalci da shigar da kowa cikin harkokin gwamnati.

A baya, Sanata Ndume ya fito fili yana sukar naɗin farko da Tinubu ya yi wanda ya ce ya nuna wariya da rashin bin tsarin kason muƙaman siyasa da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Amma a cikin wata sabuwar sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Ndume ya bayyana cewa yana ganin Shugaba Tinubu ya saurari koken jama’a kuma ya ɗauki matakin yin gyara.

Ya bayyana Tinubu a matsayin shugaba mai sauraro da karɓar gyara, wanda ke ƙoƙarin gyara kuskure idan aka nusar da shi.

Ndume ya ce babu wani shugaba da ba ya kuskure, amma abin da ke bambanta shugaba na gari shi ne yadda yake karɓar gyara cikin sauri.

A cewarsa, waɗannan sabbin naɗe-naɗen na nuna cewa yankin Arewa ba a bar shi a baya ba a harkokin mulkin ƙasar nan.

Sanata Ndume, ya ce wannan matakin zai taimaka wajen daidaita wakilci da tabbatar da cewa yankin Arewa na da muhimmanci a cikin gwamnatin Tinubu.