Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), ta ce ta kama miyagun kwayoyi na Naira miliyan biyar a Jihar Legas.
Mataimakin Kwamandan NDLEA na jihar, Mista Adetula Oluwarotimi, ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Alhamis a birnin Ikko.
- NDLEA ta kama makaho da kuturu dauke da Tabar Wiwi
- Yadda Canjin Kudi Ya Rage Harkoki A Manyan Kasuwannin Kaduna
Ya ce samamen da jami’ansu tare da hadin gwiwar sojoji suka kai yankin Mushin a Legas, sun cafke mutum 77 ciki har da wani limamin coci.
Ya ce samamen wani yunkuri na kokarin da hukumar ke yi wajen yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi da kuma tsaftace al’umma daga muggan iri.
A cewarsa, “Idan babu shaye-shayen miyagun kwayoyi, za a samu karancin aukuwar manyan laifuka.
“Kuma domin tabbatar da ba a samu aukuwar manyan laifuka ba yayin zabe mai zuwa, dole sai an ziyarci wurare,” in ji Oluwarotimi.
Ya ce miyagun kwayoyin da aka kama, ciki har da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 146.85 da ‘Methamphetamine’ giram 43.7 wanda a kiyasce kudinsu ya kai Naira miliyan biyar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewa, a watan Janairun da ya gabata ne NDLEA ta kama kimanin tan 10.827 na miyagun kwayoyi a Legas, tare da tsare mutum 88 da ake zargi da ta’ammali da kwayoyin a jihar.
(NAN)