Jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Kasa NDLEA reshen Jihar Borno, sun kama wasu dattawa biyu kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi.
Hukumar ta bayyana cewa, daga cikin ababen zargin da suka shiga hannu akwai dattijo mai shekara 70 da kuma mai shekara 65.
Femi Babafemi, Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na NDLEA ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Ya ce, an kama wadanda ake zargin ne ranar Asabar 9 ga watan Maris tare da waɗanau matasa biyu — mai shekaru 24 da kuma mai shekaru 28 — a Maiduguri da Gamboru-Ngala.
- Sanata Danso Sodangi ya riga mu gidan gaskiya
- NAJERIYA A YAU: ‘Yawan Karanta Littafai Na Sa Mutum Ya Fita Daban’
A ranar Asabar ɗin kuma, jami’an NDLEA a Karamar Hukumar Geidam da ke Jihar Yobe, sun tare wata mota kirar Golf 3 da ke kan hanyar zuwa Gagamari a Jamhuriyar Nijar, inda aka kama wani matashi mai shekaru 28 zai kai tabar wiwi mai nauyin kilogiram 24.5 ga wani dila.
Hakazalika, hukumar ta ce a ranar Talata 5 ga watan Maris, ta kwace kwali 42 mai ɗauke da kwalabe 8,400 na maganin mura mai sa maye, da ke da nauyin kilogiram 1,260 a hannun wani direba mai shekaru 29 a hanyar Katsina.
Kakakin hukumar ya bayyana cewa, sun yi nasarar damke wani dilan haramtattun ƙwayoyin da ya ɓoye kayan mayen a injin wata motar bas.
Ya ce “Sun kama wani da wiwi da ta kai kilo 5 a cikin injin motar bas mai lamba VDY 187 XA ranar Alhamis, 7 ga Maris 2024, a kan titin Gbongan-Ibadan da ke Jihar Osun bayan jami’anmu sun tsananta bincike.”
Babafemi ya ce “a yanzu haka an kama direban bas ɗin mai shekaru 35, inda aka bayar da ajiyarsa a gidan gyaran hali gabanin kammala bincike.”
A ranar Laraba, 6 ga watan Maris kuma, hukumar ta kama wata mata mai shekaru 26 da ake zargi da sayar da kayan maye.
Babban jami’in na NDLEA ya ce matar ta shiga hannu ne yayin wani samame da jami’ansu suka kai maboyarta a Osogbo, babban birnin Jihar Osun.
A Jihar Kano kuma, an kama wani matashi mai shekaru 35 da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 62 a Gadar Tamburawa, inda shi ma wani mai shekaru 40, ya shiga hannu da kwalaben maganin mura 244.
A ranar Alhamis, 7 ga watan Maris kuma, an kama wani mai shekaru 28, da ƙwayoyin tramadol guda 49,800 a kan titin Kano-Maiduguri.
A kwanakin baya ne Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Yobe, Mai Martaba Sarkin Fika, Dokta Muhammadu Abali Ibn Muhammadu Idrissa, ya bayyana shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a matsayin abin da ke rura wutar rashin tsaro a jihohin Najeriya.