An cafke shugaban wani coci a Legas kan yunkurin safarar miyagun kwayoyi da Najeriya zuwa Dubai.
Kamen ya hada da wani dalibin Kwalejin Akida da ke Ibadan da kuma wata mace guda.
- Gwamnan Yobe ya bude sabuwar kasuwar Nguru mai shaguna sama da 500
- Mun yi wa dalibai miliyan 1.1 rajistar jarabawar UTME a bana – JAMB
Jami’an Hukumar Yaki da Sha da Safarar Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ne suka kama su bayan gano miyagun kwayoyin a cikin jarkokin manja da suke shirin kaiwa Dubai a Babban Filin Jirgin Saman Murtala Muhammad, da ke Legas.
Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya fada a ranar Lahadi cewa, an damke faston da ake zargi ne a ranar Asabar bayan cafke mutum biyun da ke da alaka da shi a ranar Alhamis.
An cafke sauran mutum biyun ne tare da kulli 283 na miyagun kwayoyi da kuma giram 204 na kwayar ‘methamphetamine’ da aka dura a jarkokin manja za su kai su Dubai.
Babafemi ya ce, wadda suka kama din ta fada musu cewa faston tare da wani dansa ne suka ba ta miyagun kwayoyin don yin safararsu zuwa ketare.
Ta kara da cewa, sai da ya sa ta yi rantsuwa za ta rike sirri, wanda har kaza aka sadaukar a cikin cocin a yayin addu’ar.
A cewarta, tilasta mata suka yi ta karbi aikin bayan da ta gano abin da suke aikatawa a cocin.
Dalibin da aka kama a badakalar, ya ce an dauke shi ya rika taya budurwar aiki ne bayan an biya shi Naira miliyan biyu.
Ya ce yana bukatar kudi domin daukar nauyin karatunsa shi ya sa ya amince ya karbi aikin.
A hannu guda, NDLEA ta ce ta kama buhun tabar wiwi 130 mai nauyin ton 1.430 da aka boye a cikin wata tanka, tare da babur 13 da aka shirya yin amfani da su wajen safarar tabar a Jihar Ribas.