✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye cikin littafai ana shirin kaiwa Saudiyya

An kama ɗauri 20 na hodar iblis ɗin wanda jimillar nauyinsu ya kai giram 500 a cikin littattafan addini.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Nijeriya NDLEA, ta yi nasarar kama hodar iblis wadda aka ɓoye a cikin littattafan addini da ake shirin kaiwa Saudiyya.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Hukumar NDLEA ɗin ta fitar a ranar Lahadi.

Hukumar ta bayyana cewa ta kama ɗauri 20 na hodar iblis ɗin wanda jimillar nauyinsu ya kai giram 500 a cikin littattafan addini.

Littafan da aka ɓoye hodar iblis ɗin ana shirin kaiwa Saudiyya

NDLEA ta ce jami’anta sun gano hodar ne a yayin da suke gudanar da bincike a wani kamfanin da ke jigilar kayayyaki a Legas a ranar Talata 15 ga Afrilun 2025, yayin da yake shirin kai kayayyakin zuwa Saudiyya.

Baya ga haka, hukumar ta NDLEA ta yi ƙarin bayani game da wasu jerin nasarori da ta samu a makon da ya gabata a ƙoƙarin da take yi na daƙile fataucin miyagun ƙwayoyi.

A wani kamfanin na daban da ke jigilar kayayyaki, hukumar ta NDLEA ta ce ta kama kilo 2.8 na tabar wiwin Loud wadda aka shigar da ita ƙasar daga Amurka.

A Kano, jami’an NDLEA sun kama wani matashi ɗan shekara 22 da haihuwa da ke sayar wa ‘yan fashi da haramtattun kayayyaki a lokacin da suke sintiri a hanyar Bichi zuwa Kano.

An kama matashin ne a ranar Lahadi, 13 ga watan Afrilun, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Katsina ɗauke da kwalabe 277 na allurar pentazocine a ɗaure a cinyarsa da kuma cikin al’aurarsa.

Haka kuma, an kama wani da ake zargi mai suna Mohammed Abdulrahman Abdulaziz, mai shekaru 43, a ranar Lahadin da ta gabata a unguwar Rimin Kebe da ke Nasarawa a Kano tare da sunƙin wiwi nau’in skunk 68, wanda nauyinta ya kai kilo 30.