Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) sun kama kulle-kullen Hodar Iblis da Tabar Wiwi da dama a fadar wani basarake a Jihar Anambra.
Kwamandan NDLEA a Jihar, Muhammadu Misbahu Idris ya ce sun gano Hodar Iblis din, wacce nauyinta ya kai giram 58.5 da kuma Tabar Wiwi mai nauyin giram 13.9 ne a boye a fadar basaraken.
- Jihar Neja za ta fara ba ’yan kato-da-gora bindigogi su yaki ’yan bindiga
- ’Yan bindiga: Rundunar Sojin Kasa ta gargadi Sheikh Gumi kan lafuzansa
Sai dai bai bayar da bayani game da sunan basaraken da aka kama miyagun kwayoyin a fadarsa ko masarautar da yake jagoranta ba.
“Muna ci gaba da fadada bincike domin gano yadda aka yi aka haihu a ragaya har aka boye miyagun kwayoyin a fadar, kuma dogaran fadar suna tallafa mana sosai wurin gano ainihin dillalin kwayoyin,” inji shi.
Kazalika, kakakin NDLEA a Jihar, Odigie Charles ya ki ya bayar da cikakkun bayanai a kan lamarin.
A cewarsa, sabon shugabancin hukumar a yanzu na bukatar bayan kammala kowane irin binciken miyagun kwayoyi a kowace jiha, a bukatar rundunar ta mika rahotonta zuwa hedikwata ta kasa tukunna.
Sai dai wata majiya ta ce basaraken da ake tababa a kai shi ne Igwe na Obosi.
“An gano kwayoyin ne a fadarsa kuma muna binciken alakarsa da boye kwayoyin a fadarsa, yayin da dilansu wanda aka yi ittifakin shi ne mamallakinsu ya cika wandonsa da iska. Yanzu haka ana farautarsa ruwa a jallo,” inji majiyar.
Obosi shi ne gari mafi girma a Jihar Anambra, bayan garin Nnwei.
Garin Obosi mai tarin tsaunuka na da iyaka da Kananan Hukumomin Onitsha ta bangaren Arewa maso Yamma, da Nkpor ta bangaren Arewa maso Gabas da kuma Oba ta bangaren Kudu maso Gabas.