Tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Gali Umar Na’abba zai amsa gayyatar hukumar tsaro ta DSS cewa ya bayyana a ofishinta.
A ranar Juma’a DSS ta gayyaci Ghali Na’abba ya bayyana a ofishinta Abuja a ranar Litinin amma babu bayani game da dalilin gayyatar.
Ghali daya ne daga shugabannin sabuwar harakar siyasa ta National Consultative Front (NCFront) ta tsohon dan takarar shugaban kasa Farfesa Pat Utomi.
Jami’in Hulda da Jama’a na NCFront, Yunusa Tanko, a cikin wata sanarwa ya ce, “Ana sanar da ku cewa ranar Juma’a DSS ta gayyaci daya daga cikin shugabannin NCFront kuma tsohon Shugaban Majalisar Wakilai Ghali Umar Na’abba, bayan hirar da aka yi da shi a gidan talbijin na Channels a ranar Alhamis game da manufar NCFront na sabuwar Najeriya da za ta amfani kowa.
“Shugabanmu Ghali Umar Na’abba ya yanke shawarar amsa gayyatar kuma zai ziyarci hedikwatar DSS da ke Abuja ranar Litinin da karfe 12.00 na rana.