✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

Ɗaya daga cikin waɗanda suka kuɓuta ya bayyana yadda ya shiga hannun maharan.

Jami’an Tsaron Farin Kaya (DSS) tare da haɗin gwiwar wasu hukumomin tsaro, sun ceto wasu mutum huɗu da aka yi garkuwa da su a wani farmaki da suka kai sansanin ’yan bindiga a Jihar Sakkwato.

Ɗaya daga cikin waɗanda aka kuɓutar, Malam Umar Dankoli Kagarar Rima, ya bayyana cewa ’yan bindigar sun yi garkuwa da shi tare da jikansa mai shekara 13 a gidansa.

Ya ce ’yan bindigar sun nemi Naira miliyan 50 a matsayin kuɗin fansa, amma daga baya suka rage zuwa miliyan 10.

Malam Umar, ya ce iyalansa sun tara Naira miliyan ɗaya ta hanyar neman taimako, wanda ɗansa ya kai wa ’yan bindigar kwanaki tara da suka wuce.

Amma, lokacin da ɗansa ya kai kuɗin, sai ’yan bindigar suka riƙe shi tare da buƙatar biyan Naira miliyan 10, kafin su sake su.

A cewar Malam Umar, daga nan ne suka ci gaba da zama a hannun ’yan bindigar har zuwa lokacin da jami’an tsaro suka kai farmaki sansaninsu, tare da kuɓutar da su.

Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan sha’anin tsaro, Kanar Abdulhamid Usman (mai ritaya), ya ce nasarorin da ake samu wajen yaƙi da ’yan bindiga ba za su rasa nasaba da goyon bayan da Gwamnan Jihar, Ahmed Aliyu ke bai wa fannin tsaro ba.

Ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da goyon baya ta hanyar isar da bayanai masu muhimmanci ga jami’an tsaro domin samun ƙarin nasarori.