Hukummar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta shirya tsaf don inganta harkar kula da abokan hulda da amfani da tsarin sadarwar zamani.
Vangaren kula da harkokin abokan hulda na hukumar ya cimma matsaya a taronsa na bana mai lakabin, “Darasin Abokan Hulda a Lokacin Sauyin Gaggawa na Sadarwar Zamani” wanda ya gudana kwanakin baya a dakin taro mai daukar mutum 600 na ofishin Hukumar NCC da ke yankin Mbora a Abuja.
Mahalarta taron sun cimma matsayar ce don Hukumar NCC ta sauke nauyin kare abokan hulda kamar yadda yake a dokar Hukumar Sadarwar ta shekarar 2003 da kuma kundin dokoki da ke jagorancin ayyukan sanya ido na hukumar.
Daraktar Sashen Harkokin Abokan Hulda, Misis Felicia Onwuegbuchulam, ta ce manufar taron shi ne a inganta aiki da bunkasa hadin gwiwa da abokan hulda da bunkasa alakar sassa da gudanar da sakonni da karuwa da juna.
Ta ce yadda ake samun bunkasar kimiyya da bukatar samar da kirkira tana bukatar samar da kare abokan huldar tarho.
Kwamishinan Hukumar NCC, Mai Kula da Tattala Masu Ruwa-da-Tsaki, Adeleke Adewolu, wanda ya wakilci Farfesa Umar Dambatta ya goyi bayan abin da Onwuegbuchulam ta fadi a taron.
Adewolu ya yaba wa sashen kula da harkokin abokan hulda, inda ya dauki lokaci yana bayanin yadda za a kyautata wa abokan hulda kuma ya bukaci taron ya kawo tsare-tsare don alfanun hukumar.
An gabatar da kasidu kan yadda ake tattala abokan hulda an kuma yi muhawar tare da gudanar da dan motsa jiki a taron na kwana biyu don bunkasa ma’aikatan hukumar kan sababbin kalubalen kyautata wa abokan hulda.
An rufe taro da jawabai daga wakilan sassa takwas da ke karkashin sashen tattala abokan hulda (CAB) don sauke nauyin da aka dora wa sashen. Tattaunawar ta mayar da hankali kan gaggauta aiki don sashen CAB don magance matsalolin abokan hulda a kan lokaci kamar yadda ka’idojin Hukumar NCC suka tanada.