✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NCC ta ware Naira miliyan 500 don bunkasa makarantu a shekarar 2020

Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta ware kimanin Naira miliyan 500 don tallafi ga makarantun gwamnatin da suke da bukata ta musamman. Shugaba kuma Babban…

Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta ware kimanin Naira miliyan 500 don tallafi ga makarantun gwamnatin da suke da bukata ta musamman.

Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanawar Hukumar NCC, Farfesa Umar Garba Dambatta ne ya bayyana haka a Kano kwanaki baya a bikin bude taron kwana biyu da Cibiyar Kimiyyar Bayanai da Bunkasawa ta CITAD ta shirya.

Farfesa Dambatta ya ce  kudin wanda za a samar da shi a cikin shekarar 2020 wani bangare ne na tallafin da hukumar ke bayarwa kuma za a iya samunsa yayin da makarantar da ke bukata ta rubuto bukatarta.

“NCC ta ware kudin tallafi na shekarar 2020 wanda ya kai kimanin Naira miliyan 500 hakan ya hada da tallafin da muke bayarwa a bangarori daban-daban musamman ma ga jami’o’i da kwalejojin kimiyya da fasaha da kwalejojin gwamnati da makarantun sakandire amma wannan wani tallafi ne na musamman wanda aka ware don gyaran makarantu da samar musu da abubuwan zama da gina rijiyoyin burtsatse a makarantun da ke bukata da makamantansu”.

Ya bayyana cewa  kudin an ware su ne don makarantun gwamnati kawai  na jihohi da na tarayya. Don samun tallafin Farfesan ya ce “Mun tsara matakan samun kudin  daga ciki shi ne  ya zama wajibi makarantar ta rubuto abin da take bukata  sannan za mu je mu gani da kanmu don tantance shin ya kamata  ta samu tallafin kuma ya dace da ci gaba da bunkasar makarantar”.

Da yake gabatar da jawabi mai taken: “Tsarin Intanet din da muke bukata da rawar da mai sanya ido zai taka”, Farfesa Dambatta ya kare Hukumar daga zargin da ake yi mata a kafafen sa da zumunta wanda yake barazana ga tsaron kasa inda ya ce  Hukumar NCC ba ta da karfin sanya ido kan abubuwan da ke yaduwa a yanar gizo.

Ya bayyana cewa sanya ido kan bayanan yanar gizo nauyi ne na Hukumar da ke sanya ido kan Gidajen Yada Labarai ta NBC inda ya shawarci matasa su ci moriyar damarmakin da ke kafafen sa da zumunta don amfanin kansu da bunkasar tattalin arziki tare da nisantar barnata shi.

“NCC ba ta sanya ido kan kimiyya da fasaha da kuma manhaja kamar manhajar OTT kamar kafar sa da zumunta ta Whatsapp da Google da Facebook, da Wechat da Skype da makamantansu. Ba ma sanya ido kan wadannan kodayake akwai cece-kuce kan ya kamata Hukumar NCC ta rika sanya ido a kansu amma a duniya baki daya akwai kasashen kadan da ke sanya ido kan manhajar OTT saboda tasirin da suke da shi kan dan’adam saboda yadda suke taimakawa ’yan kasa babu shakka wadannan tallafi za su iya kasancewa masu gyarawa ko kuma batawa, za ka yi mamakin kasashen da ke bin tafarkin damokradiyya idan suka yi yunkurin hana wadannan abubuwa irin sukar da za su sha.

“Ya kamata gwamnati ta yi aikinta sosai wajen bayyana dalilin da ya sa za a sanya ido kan manhajar OTT kuma ta yaya za a sanya idon, wannan ya janyo dalilin da kungiyar sadarwar tarho ta duniya da ke sanya ido kan sadarwar tarho take daukar lokacinta ta fitar da hanyoyin da za a sanya ido kan manhajar OTT,” inji Danbatta.