Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) a ranar Alhamis ta kara tsaurara tsaro a bangarenta domin kariya ga masu amfani da bangaren sadarwa a kasar nan.
Hukumar ta nuna rashin jin dadi kan amfani da kafafewa sadarwa wajen yaudarar mutane ta Intanet a Najeriya.
Daraktan Bangaren Harkokin Al’umma a Hukumar NCC, Misis Felicia Onwuegbuchulam ce ta bayyana haka a lokacin bude taro na 53 mai taken “rage barna ta yanar gizo: Amfanin masu amfani da yanar gizon” a garin Oyo da ke Jihar Oyo.
Ta ce hukumar tana duk abin da ya kamata don yaki da ta’asar.
Daraktar wadda ta samu wakilcin Alhaji Ismail Adedigba, ta ce “Ya kamata a san cewa hukumar tana kokarin kare yadda ’yan Najeriya za su ci gaba da amfani yanar gizo yadda ya kamata, musamman kan wadanda tunaninsu su yi amfani da yanar gizo ta haramtacciyar hanya. Masu neman yaudarar mutane ta hanyar sadarwa. Ta’addancinsu yana karuwa ne ita kuma hukumarmu tana kokarin wayar da kai ga masu amfani da yanar gizo,”
Ta karfafa niyyar hukumar wajen wayar da kan abokan hulda kan hadarin da ke tattare da yanar gizo da sa ido ga hukumar wajen muhimman bayanai don kawar da ta’addanici a yanar gizo a lokacin da yake magana kan muhimmancin taron.
Ya ce abu guda da NCC ta gano, kuma ta fuskanta domin samaun mafita ga harkar sadarwa da bayanai don gamsar da abokan hulda a lokacin da bukata ga masu sadarwa.
“Tunda muka fara shirin shekarun baya, mun yi fama da abubuwa daban-dabam, wanda muka samu hanyoyi da muka yi magana da hukumar sadarwa. Kuma wannan shi ne ya sa muka inganta yanayin sadarwarmu domin kudin da muka sa domin ci gaban kasuwancinmu.”
Basharun na Masarautar Oyo, Chif Yusuf Ayoola wanda ya wakilci Sarkin Oyo, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi III a taron ya bukaci Hukumar NCC ta rika yawan irin wadannan tarukan na ganawa da abokan hulda, inda ya ce ya kamata a rika yi duk wata domin koyar da masu amfani da abokan huldarsu yadda za su kare kansu daga fadawa cikin yaudarar yanar gizo.
Shugaban kungiyar Wheel of Hope, kungiya mai kare hakkin abokan hulda Mista Jide Abdul-Azeez wanda mai jawabi a wajen taron ya bayyan hanyoyi da dama da ake amfani da su wajen yaudarar mutane a yanar gizo, sannan ya bukaci masu amfani da yanar gizo su bi a hankali wajen fitar da bayanan sirrinsu ga wadanda ba su sani ba.