Hukumar Kula da Kafofin Sadarwa ta Kasa (NCC) ta musanta labaran da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ta ba kamfanonin sadarwa umarnin toshe hanyoyin sadarwa a Jihar Katsina.
Daraktan Yada Labarai na Gwamna Aminu Bello Masari, Alhaji Abdul Labaran ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Katsina ranar Litinin.
- Muna roka wa Najeriya shugaba kamar Buhari a 2023 —Umahi
- Matakan da muka dauka sun hana ’yan bindiga sakat a Zamfara – Matawalle
Ya ce Shugaban Hukumar ta NCC, Farfesa Umar Garba Danbatta wanda ya yi magana da Gwamnatin Jihar ya bayyana labarin a matsayin na kanzon kurege.
“Danbatta ya kuma ce takardar wacce take yawo a kafafen sada zumunta na zamani an jirkita wacce suka fitar a kan Jihar Zamfara ce a makon jiya,” inji shi.
Daga nan sai Alhaji Labaran ya shawarci jama’a da su yi watsi da labarin a matsayin wanda ba shi da tushe ballantana makama kasancewar ba daga NCC ya fito ba.
Idan za a iya tunawa, NCC a makon da ya gabata ta umarci dukkan kamfanonin sadarwa su katse dukkan hanyoyin sadarwa a Jihar Zamfara a matsayin daya daga cikin irin matakan da ake dauka wajen yaki da ayyukan ’yan bindiga a Jihar.