✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nazarin littafin Kemestare (An Introductory Chemistry Tedt In Hausa Language)

Mawallafi: Dokta Mikailu Maigari KashimbilaMai nazari ko sharhi: Isiyaku MuhammedFarashi: ba a fada ko rubuta baBugun farko: 2006Kamfanin dab’i: Enterprises for scientific and technological publications…

Mawallafi: Dokta Mikailu Maigari Kashimbila
Mai nazari ko sharhi: Isiyaku Muhammed
Farashi: ba a fada ko rubuta ba
Bugun farko: 2006
Kamfanin dab’i: Enterprises for scientific and technological publications in Hausa language. Gidan Mariya dantata, hanyar BUK, kofar Kabuga, Kano.

Littafin Kemestare na daya littafi ne wanda Dokta Mikailu Maigari Kashimbila ya wallafa a cikin harshen Hausa. A cikin littafin, mawallafin ya rairayo muhimman al’amura da suka shafi kimiyya don amfanin daliban sakandare da masu karatun sharar fagen shiga jami’o’i.
Littafin ya kunshi darussa guda goma sha biyu a cikin shafuka 144, sannan kuma a kowane darasi, mawallafin ya bayar da ayyukan yi domin auna fahimta.
A darasi na daya, mawallafin ya yi bayani ne a kan abin halitta wanda ake kira “Matter” da kuma siffar kwayar zarra, a darasi na biyu kuma mawallafin ya yi bayani ne akan aune-aune, inda ya yi bayanin ma’aunai da kuma yadda ake amfani da su. A darasi na uku, ya yi bayani ne a kan Molakul, wato “molecule” da kuma lambar Abogadro, haka nan kuma a darasi na hudu, ya yi bayani a kan canjin kamanni na ma’adinai in aka gauraya su, wato abin da ake nufi a Turance, “physical and chemical change.”
 A darasi na biyar kuma mawallafin ya yi bayani ne a kan cigaba da bayanin darasi na biyu, wato aune-aunen abubuwa. A darasi na shida kuma mawallafin ya yi bayani ne a kan ka’idojin da suka danganci, iska wato ‘Gass laws.’  A darasi na bakwai kuma ya yi bayani ne a kan ka’idojin da suka danganci hade-haden ma’adinai. A darasi na takwas kuma ya yi bayani ne a kan taswirar ko tsarin lantarori wato electronic configuration, inda ya yi bayanin wasu ka’doji kamar ta su Paulli game da samuwar lantarori biyu a gurbi guda. A darasi na tara kuma mawallafin ya kawo bayani ne a kan shirya Elamomi cikin jadawali, wato the periodic table. Haka nan kuma a darasi na goma, mawallafin ya yi bayani a kan yadda Elamomi ke haduwa a samu sababbin ma’adinai. A darasi na goma sha daya kuma ya yi bayani ne a kan lambar Haduwa oksijin, wato odidation number sannan kuma a darasi na goma sha biyu kuma darasi na karshe mawallafin ya yi bayani a kan daidaita jumlolin kimiyya wato balancing chemical ekuations.
Abubuwan da dalibai za su karu da shi daga littafin:
1. Saukin fahimta.
Littafin an rubuta shi cikin harshen Hausa ne, domin ya saukake wa dalibai wahalar fahimta. Domin ilimin Kemestare na da matukar muhimmanci ga harkar kimiyya, sannan kuma wani ginshiki da ya sa duk wani dalibi yana bukatar ya sanshi matuka. Hakan ya sa littafin ya kawo nesa kusa domin kuwa an saukake bayanan yadda duk wani mai jin Hausa zai fahimci ilimin cikin sauki ba tare da wahalar fahimtar yaren Ingilishi ba. Misali a  shafi na goma sha hudu, mawallafi ya yi jadawali, inda ya kawo kalmomin kimiyya sannan kuma ya fadi ma’anarsu da harshen Hausa. Wannan zai taimaka sosai wajen fahimtar wadannan kalmomin da kuma fahimtar duk inda aka yi amfani da su.
A darasi na biyu, mawallafin ya yi bayani a kan yadda ake lissafin aune-aune cikin sauki, ganin yadda lissafi ke da wahalar gaske, wannan littafin zai taimaka wajen sanin yadda ake yin aune-aune cikin sauki. Haka nan ma a darasi na uku, mawallafin ya yi bayani a kan wasu nau’ukan lissafai masu wahalar ganewa, inda ya bayyana su cikin sauki, hakan zai sa duk wanda ke jin Hausa ya fahimci lissafin cikin sauki, musamman a bangaren sarrafa lambar Abogadro. Sannan kuma darasi na tara, mawallafin ya yi bayani cikin sauki yadda za a fahimci shirya elamomi cikin jadawali wato periodic table. a cikin darasin akwai cikakken bayanin yadda aka shirya elamomin cikin jadawali na Dmitry Mendeleb da kuma tsarin shiryawa na zamani, sannan kuma a shafi na 98 da na 99 duk a cikin darasi na tara mawallafin ya kawo jadawaloli guda biyu, wadanda ya sanya wa suna jadawali na biyu da jadawali na uku. A cikin kowane jadawali an nuna elamomi da kuma yadda ake tsara su da kuma taswirar su cikin sauki ba tare da wahala ba. Haka nan dai mawallafin ya yi kokari wajen saukaka ilimin Kemestare a cikin Hausa.
2. Cikakken bayani.
Haka nan kuma littafin ya kunshi cikakken bayani a karamin littafi. Mawallafin ya yi kokari sosai wurin dunkule tarin ilimin Kemestare a cikin karamin littafi, domin a fahimta ba tare da bata lokaci ba. Saboda daukacin littafin ya kunshi shafuka 144 ne kawai. Wannan zai taimaka, musamman ga dalibai masu rauni a harshen Ingilishi. Saboda a wannan zamani duk wanda zai koyi fannonin ilimi dole sai ya hada da Turanci, inma Ingilishi ko Faransanci.
3. Fassarar Kalmomi masu wahalar fahimta.
Yawancin kalmomin kimiyya kalmomi ne wadanda ba a fahimtar su sai dai kawai a haddace su ba tare da sanin ma’anarsu, kuma kowane ilimi yana bukatar cikakkir fahimta domin amfani da shi. Wannan shi ya sa ko Alkur’ani mai girma ake fassara shi domin a fahimceshi sannan kuma a yi aiki da shi, domin idan ba a fahimce shi ba, zai yi wuya a yi aki da shi yadda ya dace. Rashin fahimtar harshen kimiyya yasa ba a fahimtar kimiyya yadda ya kamata, wanda hakan ya sa muka zama koma baya a harkar ilimin kimiyya. Amma cikin wannan littafin, mawallafin ya yi kokari matuka wajen fassara  kalmomin kimiyya tare da yin bayani cikin harshe ma fi sauki domin saukake fahimta, wanda wannann fahimtar za ta taimaka wa ci gaban kimiyya, musamman a yankin Arewacin Najeriya da kuma sauran wuraren da ake Magana da harshen Hausa. Sannan kuma duka ya yi nazarin littafin da kyau. Koda daga baya ya dauko na Turancin Ingilishi yana nazari zai ga kamar ana yi masa fassara ne kawai. A karshe ina bai wa dalibai ‘yan sakandare da kuma wadanda suke sharar fagen shiga jami’o’I da malamai shawara da su mallakin wannan littafin domin zai taimaka matuka. dalibai su tabbata sun yi nazarin littafin da masana fannin domin shi ne zai taimaka musu wajen fahimtar littafin da kyau. Saboda ba a yin karatu sai da malami. Haka nan kuma littafin zai taimaka wa masu karatun share fagen ne domin idan suka shiga jami’a za su fahimci ilimin Kemestare cikin sauki, ta yadda za su rinka ganin karatun a saukake, tunda sun fahimce shi sosai a harshen da suka fi iyawa. Sai  kuma malamai, su ma littafin zai taimaka musu wajen koyar da ilimin Kemestare ta hanyar samun saukin kwatance mai nisa da kuma koyar da irin lissafin da ake amfani da shi a fannin kimiyyar Kemestare.