Kasancewa mai azumi yana neman kusanci da Allah ne da rokonSa shiriya da sauran alherai, sai Allah Ya nuna cewa Shi Makusanci ne ga masu kiranSa, amma da sharadin su nemi karbawarsa bayan sun yi imani da Shi. Akwai Hadisai da dama da suke da alaka da abin da ayar take magana, daya daga ciki shi ne Hadisin Abu Huraira (RA) da ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Lallai Allah Yana cewa: “Ina inda bawaNa yake zatoNa, kuma ina tare da shi idan ya kiraNi.” (Muslim ne ya ruwaito)
Fa’idojin wannan aya sun hada da:
1. Shar’antawa da mustahabbancin yin addu’a. (Taisirul Karimur Rahman shafi na 69).
2. Kusancin Ubangiji ba ya lizimtar cudanya, a’a Makusanci ne a cikin daukaka.
3. Makaruhancin daga sauti a lokacin ibada, in ba ya ga talbiyya da kiran Sallah da ikama. (Aisarut Tafsir, Mujalladi na 1 shafi na 165).
4. Wajibcin amsawa da mika wuya ga umarnin Allah. (Jami’u Ahkamil kur’an Mujalladi na 2 shafi na 313)
5. Amsa kira da bin umarnin Allah yana gadar da shiriya da dacewa. (Taisirul Karimir Rahman shafi na 69).
Aya ta gaba kuma sai ta ce:
“ An halatta a gare ku, a daren azumi, yin jima’i zuwa ga matanku, su tufa ne a gare ku, ku ma tufa ne a gare su, Allah Ya sani, lallai ku kun kasance kuna yaudarar kanku. Saboda haka Ya karbi tubarku, kuma Ya yafe muku. To yanzu ku rungume su, kuma ku nemi abin da Allah Ya rubuta muku. Kuma ku ci ku sha har silili fari ya bayyana a gare ku daga silili baki daga alfijir, sannan ku cika azumi zuwa ga dare. Kuma kada ku rungume su alhali kuna masu I’itikafi a cikin masallatai. Wadannan iyakokin Allah ne: don haka kada ku kusance su, kamar haka ne Allah Yake bayyana ayoyinSa ga mutane: tsammaninsu, za su yi takawa. “k:2”187)
Allah Mafi girma! Dubi yadda a ayar farko ya rufe ta da takawa, haka kuma dubi yadda ya rufe aya ta karshe da batun takawa bayan Ya yi magana kan abubuwan da aka halatta ga mai azumi da dare. Wannan yana nuna kashin bayan yin azumi shi ne a samu takawa.
Fa’idojin da wannan aya take koyarwa, sun hada da:
1. Halaccin ci da sha da jima’i a dararen azumi bayan ya kasance haramtacce idan aka yi barci a baya. (Jami’ul Bayan, Mujalladi na 3 shafi na 464).
2. Lokacin azumi yana farawa ne daga ketowar alfijir zuwa faduwar rana. (Aljami’u Li’ahkamil kur’an, Mujalladi na 2 shafi na 319).
3. Ana son yin amfani da kinaya maimakon bayyanawa balo-balo a abin da akwai kunya a cikinsa. (Aljami’u Li’ahkamil kur’an Mujalladi na 2 shafi na 315)
4. Shar’anta I’itikafi a cikin Ramadan da yankewa daga mutane domin yin ibada. Kuma mai I’itikafi bai halatta a gare shi ya ji dadi da matarsa har sai lokacin I’itikafinsa ya kare. (Tafsirul kur’anil Azim, Mujalladi na 1 shafi na 213).
5. Haramcin keta hurumomin shari’a da ketare haddodinta. (Tafsirul kur’anil Azim, Mujalladi na 1 shafi na 213)
6. Bayyana makasudin saukar da shari’o’i da sanya haddodi, wato takawa ga Allah Madaukaki. (Ruhul Ma’ani, Mujalladi na 2 shafi na 69).
Nazari kan ayoyin da suka yi magana kan azumin Ramadan (2)
Kasancewa mai azumi yana neman kusanci da Allah ne da rokonSa shiriya da sauran alherai, sai Allah Ya nuna cewa Shi Makusanci ne ga masu…