A 1964 ce kamfanin wallafa na ‘Kazi Publishing Company’ da ke kasar Masar ya buga shahararen littafin nan na Ma’alimun Fid-Darik, na Shahid Sayyid Kutub Ibrahim; littafin da Gwamnatin Masar, karkashin jagorancin Jamal Abdul-Nasir ta ce shi ne kundin juyin-juya-halin Musulunci, wanda ta ce yana barazana ga dorewar mulkin mahukuntan kasar. Wannan ne ya sanya aka gurfanar da marubucinsa a kotu kuma aka yanke tare da zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya gare shi, a ranar 29 ga Agustan 1966.
Littafin Mu’alim Fid-Darik, ana sanya shi cikin fitattun littattafan da aka rubuta a karni na 20 saboda abin da ya kunsa na kyakkyawan tunanin Musulunci da hanyoyin gyaran al’umma Musulma wajen dawo da ita bisa tsarin Musulunci da Annabi (SAW) ya kafa a duniya baki daya.
Littafin, wanda ke dauke da babi-babi har 12, an buga shi a shafi 160. A gabatarwar littafin, Sayyid Kutub ya bude shi da nuni ga yadda jinsin dan Adam yake neman karewa karkaf, ba ta hanyar hallaka ba, a’a ta hanyar canja tunanin dan Adam daga manufar halittarsa da Allah (SWT) Ya yi, zuwa bautar tunanin Yammacin Turai. Kamar yadda yake fadi cewa: “A yau duniya gaba dayanta tana rayuwa ne cikin Jahiliyya ta gaske, wadda duk ginshikan rayuwa da tsare-tsare ke bubbugowa daga gare ta, Jahiliyya wadda duk kayayyakin jin dadi da kere-kere masu burgewa ba su dade ta da komai ba. Wannan Jahiliyya ta doru ne a kan adawa da jagorancin Allah a bayan kasa da kuma wata siffa mafi girma daga cikin siffofinSa, wato hukunci. A haka sai ta sanya sashensu zama iyayengiji ga sashe, kuma ba ta bayyana ta siffa sassauka irin ta Jahiliyyar farko da muka sani ba.”
A Babi na Farko, Shaihin malamin ya yi bayani a kan yadda karnin farko ya kasance; wato zamanin Manzon Allah (SAW), wanda ya canja al’ummar farko daga Jahiliyya zuwa tsarkakakkiyar al’umma. Kamar yadda yake cewa: “Manzon Allah (SAW) ya yi nufin gina jama’a ce mai tsarkakakkiyar zuciya, hankali, ra’ayi da fahimta, wadda gina ta ya tsarkake ta daga tasirin wani abu idan ba tsarin Ubangiji ba, wanda yake shi ne Alkur’ani.”
A Babi na Bakwai, Shaihin malamin ya nuna cewa ba wani tsari ne wayewa ba, idan ba Musulunci ba, inda yake cewa: “Al’ummar Musulma ita ce al’umma da ke dabbaka Musulunci a akida da ibada, a shari’a da tsari, a halaye da dabi’a. Sannan al’umma jahila ita ce wadda ba ta dabbaka Musulunci, ba ta hukunci da shi a akidance da fikirance, ba ta hukunci da kimominsa da tsarinsa da shari’o’insa da dabi’unsa da halayensa.” Ya ci gaba da cewa: “Al’umma Musulma ba ita ce wadda wadansu gungun mutane ke kiran kansu Musulmi ba, alhali shari’ar Musulunci ba ita ce dokokin al’ummar ba, ko da suna Sallah, suna azumi suna hajjantar Dakin Allah. Haka kuma al’umma Musulma ba ita ce wadda mutane ke kago irin nasu Musuluncin da wani abu koma bayan abin da Allah da ManzonSa suka tabbatar ba, sa’annan su ba shi sunan ci gababben Musulunci.”
A Babi na Karshe da ya yi masa take da: “Wannan ita ce hanyar,” ya yi nuni da yadda dawagitai ke amfani da karfi ta hanyar barazana ko dandana wa masu kira zuwa ga Musulunci azaba, ta hanyar amfani da wuta kamar dai yadda aka yi wa As’habul Ukhdud, ko dauri, ko kora daga kasa, ko kuma kisa gaba daya amma dai tabbas nasara gare su take, haka nan hallaka da tabewa ta tabbata ga azzalumai.
Akwai abubuwa masu yawa na tunanin Musulunci da littafin ya kunsa da ba za mu iya kawo su a nan ba. Wannan ce ta sanya shekara daya bayan buga littafin, mahukuntan kasar Masar suka sa aka kama Sayyid Kutub tare da kashe shi ta hanyar rataye shi a 1966. Wannan ne kuma ya sanya aka yi masa lakani da ‘Ash-Shahid’ wato wanda aka kashe a tafarkin Allah.
Haka kuma duk da yadda mahukunta kasar suka haramta littafin, an samu tabbacin cewa littafin ya zama mafi soyuwa a yankin Larabawa da duniya baki daya, inda aka ce an buga shi har kusan sau dubu biyu, sannan an fassara shi da Ingilishi da sunan ‘Milestone.’ Mu ma a nan Najeriya, an fassara littafin da Hausa da sunan ‘Alamomi A Kan Hanyar Da’awar Musulunci,’ wanda Sheikh Abubakar Mujahid, Shugaban Kungiyar Jama’atu Tajdidil Islamiy da Malam Ibrahim Musa Editan jaridar Al-Mizan suka yi a shekara ta 1415 Bayan Hijira.
A ranar 29-08-1966, Gwamnatin Jamal Abdun-Nasir ta zartar da hukuncin kisa ga fitacce kuma shahararren malamin na addinin Musulunci kuma jagoran Kungiyar ’Yan uwa Musulmi, Sayyid Kutub Ibrahim.
An haifi Sayyid Kutub Ibrahim a ranar 9 ga Oktoba 1906, a garin Musha na kasar Masar. Kwararren marubuci, malamin Musulunci kuma jagora a Kungiyar Gwagwamayar Musulunci (Ikhwanil Muslimin). Marubucin shahararre ne a fagen tafsirin Kur’ani da littafin Tafsirinsa mai ‘Fi-Zilalil Kur’an’ da kuma ‘Ma’alimun Fid-Darik’ wanda sakamakon rubuta shi Gwamnatin kasar Masar ta sa aka kashe shi ta hanyar ratayewa.
Kamar malamansa, Hasan al-Bannah, Sheikh Muhammad Abdu da Rashid Rida, shi ma ya tasirantu da fahimtar Musulunci da kyamar Turawan Yamma wajen yaki da akidun Musulunci.
A shekarun 1948 zuwa shekarar 1950, Sayyid Kutub ya halarci Jami’ar Colorado a Amurka. A can ne ya rubuta littafinsa ‘Al-Adala al-Itijma’iyya fil-Islam’ wanda aka buga shi a 1949 a kasar Amurka. Haka kuma ya yi aiki a Jami’ar Colorado da kuma Jami’ar Stanford, haka kuma ya ziyarci mafi yawan manyan biranen kasar Amurka. Ya karanci zamantakewar Amurka kamar yadda ya bayyana bayan dawowarsa, a mukalarsa mai taken ‘Amurka Allati Ra’aitu,’ wato ‘Amurkar Da Na Gani Da Idona.’
Bayan dawowarsa Masar a wajejen 1950, ya bar aikin gwamnati, ya shiga kungiyar da Imam Hasan al-Banna ya kafa, ‘Ikhwanul Muslimin.’ Ya zama babban Editan Jaridar Ikhwan kuma babban dan Majalisar Shura na kungiyar. Tun daga lokacin ya yi ta karo da mahukunta Masar, karkashin jagorancin Jamal Abdun-Nasir, bayan yunkurin kashe Jamal din da wadansu masu kishin addini suka yi a 1954; ya jefa Kutub da wadansu da yawa daga ’ya’yan Kungiyar Ikhwan a kurkuku, inda ya shafe tsawon shekara uku a daure. A lokacin zamansa a kurkuku ne Kutub ya rubuta fitattun littattafansa, Tafsirin Alkur’ani ‘Fizilalil Kur’an (In the Shade of Kur’an)’ da kuma ‘Ma’alimun Fid-Darik (Milestone)’ wanda a cikinsa ya bayyana manufofi da kudurce-kudurcen Musulunci da siyasa, ya kuma kalubalanci manufofin Turawan Yamma. Littafin da gwamantin ta ce shi ne kundin manufofin juyin-juya-hali, inda ta haramta shi, kuma bayan fitowarsa da wata takwas kacal, aka kara gurfanar da shi a gaban kotu; inda aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar ratayewa. A ranar 29 ga Agusta 1966 kuma aka rataye shi.
Muna rokon Allah (SWT) Ya yi jinkai ga Sayyid Kutub Ibrahim, Ya karbe shi a matayin Shahidi, kamar yadda muke rokonSa Ya sanya mu yi shahada a karshen rayuwarmu. Allah Ya ba mu dacewa, amin.
Malam Aliyu ya rubuto wannan sharhi ne daga Kano