✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Nau’ikan abincin da ya kamata mai Hawan Jini ya rika ci

Cin abinci mai gina jiki da kuma salon rayuwa mai armashi na taimakwa wajen kare kai daga kamuwa da lalurar hawan jini. Masanin abinci mai…

Cin abinci mai gina jiki da kuma salon rayuwa mai armashi na taimakwa wajen kare kai daga kamuwa da lalurar hawan jini.

Masanin abinci mai gina jiki, Paul Okoh ne ya bayyana haka a matsayin wani bangare na bikin Ranar Yaki da Cutar Hawan Jini ta Duniya ta 2022, inda ya shawarci mutane su kula da abincin da suke ci don kauce wa kamuwa da cutar.

Masanin ya lissafo wasu nau’ukan abinci da ’ya’yan itatuwan da suka dace a yawaita cin su don su zame wa jiki garkuwa daga matsalar hawan jini.

Mista Okoh ya ce ayaba da gwaba da mangwaro  da gwaza baki dayansu suna da matukar tasiri wajen yaki da hawan jini bayan an kamu kuma kariya ce daga kamuwa da shi saboda suna kunshe da muhimman sinadarai.

“Sai kuma abinci masu karancin kitse da a kan samu a jikin dabbobi, su ma suna da tasiri wajen yaki da lalurar hawan jini.

“Yawan aiki babu hutu da salon rayuwa mara armashi da rashin kiyaye ladubban cin abinci na daga cikin abubuwan da kan haifar da hawan jini.”

Daga nan, ya nuna bukatar da ke akwai a rika lura da yanayin bugun jini lokaci-lokaci, saboda riga kafi ya fi magani.

Ya nusar da al’umma kan a sani cewa, hawan jini shi ne kan gaba wajen haifar da ciwon zuciya, ko mutuwar barin jiki.

Ranar 17 ta Mayun kowace shekara ce Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ware domin wayar da kai game da cutar hawan jini da kuma yaki da ita.

Bisa bayanin WHO, hawan jini na somawa ne daga lokacin da bugun jini ya kai matakin 140/90 ko sama da haka.

Hukumar ta ce lalurar hawan jini ta zama abin damuwa matuka, saboda tana iya haifar da cututtuka da dama, kamar bugun zuciya da shanyewar barin jiki da cutar koda da sauransu.

Ta kara da cewa, jama’a da dama na fama da wannan lalurar ba tare da sun san da hakan ba, har sai bayan ta yi tsanani, shi ya sa ake ganin ta a matsayin mai kisan mummuke.