✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda wasan Najeriya da Afirka ta Kudu ya yi ajalin mutum 5 saboda faɗuwar gaba

Akalla an samu mutum biyar da suka mutu sanadiyyar faɗuwar gaba da bugun zuciya yayin kallon wasan Najeriya da Afirka ta Kudu.

Masu iya magana na cewa ana bikin Duniya ake yin na Ƙiyama, hakan kuwa ce ta kasance a ranar Larabar da ta gabata ga wasu ’yan Nijeriya da ajali ya katse musu hanzari.

A ranar Larabar ce dai tawagar kwallon kafa ta Najeriya wato Super Eagles, ta fafata ta tawagar kwallon kafar Afirka ta Kudu wato Bafana-Bafana.

An dai yi karon battar ne tsakanin kasashen biyu a matakin wasan kusa da na ƙarshe na Gasar Kofin Nahiyyar Afirka ta AFCON da ke gudana a Ivory Coast.

A ƙarshe dai Najeriya ce ta zama zakara, bayan ta kai su ga bugun faneratin da ta yi nasara da ci 4-2, saboda har aka buge mintuna 120 ƙarfi ne ya zo ɗaya inda aka tashi 1-1.

Sai dai a yayin da ake tsaka da wannan wasa da ya ɗauki hankalin ɗimbin jama’a, wasu kuwa ana zargin shi ne ya zama silar ajalinsu a dalilin faɗuwar gaba.

Aminiya ta ruwaito cewa, an samu wani mutum, Mikail Osundiji mai shekaru 43 wanda ya rasu yana kallon wasan a wani gidan kallo da ke yankin Olomoore na birnin Abeokuta da ke Jihar Ogun.

Ana dai zargin fargaba da bugawar zuciya ta yi ajalin mutumin a daidai lokacin da alƙalin wasan ya soke kwallon Najeriya ta biyu wadda dan wasan gaba, Victor Osimhen ya jefa, sannan ya bai wa Afirka ta Kudu bugun fanareti a yayin da sakamakon wasan yake ci 1-0.

Wata ’yar uwar mutumin dai ta ce lafiya ƙalau ya fita kallon wasan, amma a daidai lokacin da murnar tawagar Super Eagles ke komawa ciki, sai kuwa ya sunkuyar da kansa ya faɗi wanwar a kasa, lamarin da ya ɗauki hankalin sauran masu kallon wasan suka garzaya da shi wani asibiti mafi kusa, inda a nan likitoci suka tabbatar da cewa ya cika.

Tuni dai an yi jana’izarsa bisa koyarwar addinin Islama a ranar Alhamis kamar yadda ’yar uwarsa mai suna Nofisat ta tabbatar tana mai neman gwamnati ta kawo musu ɗauki saboda ya tafi ya bar masu buƙatar kulawa da suka haɗa da mahaifa da iyalinsa ciki har da ’ya’ya biyu.

Wannan dai, yana cikin jerin mutanen da ƙarar kwana ta cimma suna tsaka da kallon wasan, inda mun samu cewa akwai tsohon Babban Darektan Hukumar Raya Neja Delta, Dokta Cairo Ojougboh wanda shi ma faɗuwar gaba ta zamo silar ajalinsa.

Hakan ne ƙunshe cikin wata sanarwa ba da tabbaci da Gwamnan Delta, Sheriff Oborewori ya fitar ta hannun Babban Sakataren Labarai na Fadarsa, Mista Festus Ahon a ranar Alhamis.

Ahon ya ce Gwamna Oborewori ya jajanta wa iyalan marigayin da Masarautar Agbor da kuma jam’iyyar APC dangane da rasuwar fitaccen dan siyasar.

Kazalika, akwai wani mataimakin babban jami’in kula da harkokin kuɗi na Jami’ar Jihar Kwara (KWASU), Alhaji Ayuba Olaitan Abdullahi, wanda shi ma ya ce ga garinku nan a dalilin kallon wasan da ake hasashen ya fi kowanne zafi da ɗaukar hankali a duk cikin wasannin da aka fafata a gasar ta AFCON.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, Alhaji Ayuba ba tare da ya yi aune ba ya tsinci kansa a cikin yanayi na rashin lafiya yana tsaka da kallon wasan a wani gidan kallo da ke yankin Sango a birnin Ilorin na Jihar Kwara.

Wata majiya ta buƙaci a sakaya sunanta, ta ce Alhaji Ayuba ya kalli wasan har zuwa lokacin da ake shirin soma bugun fanareti, inda ya ce “zai tafi gida ya kwanta saboda jiri ya fara ɗaukarsa ba tare da sanin cewa ashe jininsa ne ya hau ba.

“Yana zuwa gida kuwa sai ya zube a kasa, inda aka yi gaggawar miƙa shi wani asibiti a Sango, amma aka tura su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilorin, sai dai kafin a duba shi ma ya riga ya cika,” a cewar majiyar.

Jami’ar hulɗa da al’umma ta jami’ar, Dokta Saedat Aliyu ta tabbatar da mutuwar Alhaji Ayuba cikin wata sanarwa da fitar tana mai roƙon Allah Ya jikansa Ya sa Aljannatul Firdausi ce makomarsa.

Shi ma dai wani matashi mai yi wa kasa hidima a garin Numan da ke Jihar Adamawa, irin haka ce ta kasance da shi yayin kallon wasan na ranar 7 ga watan Fabarairu.

Wakiliyarmu daga birnin Yola, ta ruwaito cewa matashin mai suna Samuel ya yanke jiki ya faɗi ne jim kaɗan gabanin soma bugun fanareti.

Samuel wanda dan asalin Jihar Kaduna ne, an yi gaggawar miƙa shi wani Babban Asibiti amma kafin wani lokaci kaɗan mai yankan ƙauna ta yi masa halin da ta saba.

Shugaban Hukumar Hidimar Kasa na Jihar Adamawa, Mista Jingi Dennis, ya tabbatar da mutuwar Samuel wadda ya ce ta ɗimauta su.

Ya ce kamar yadda wasu abokan kallon kwallo suka ba da shaida, Samuel ya sanar musu da cewa ba ya son yana kallon kwallo ta kai ga bugun fanareti.

Sun ce ana tsakar kallon ne kuwa sai ya sunkuyar da kansa daga bisani kuma ya zube a kasa wanwar

Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Adamawa, SP Suleiman Yahya Nguroje, amma hakan bai samu ba.

A birnin Bouake na kasar Ivory Coast da ke karɓar bakuncin gasar ta AFCON, an samu wani hamshakin dan kasuwa dan Najeriya mai suna Osundu Nwoye wanda shi ma ya yanke jikin ya faɗi yana tsakar kallon wasa.

Cikin wani saƙo da wani mai suna Chukwudi Iwuchukwu ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce attajirin dan asalin Jihar Anambra masoyin kwallon kafa ne na haƙiƙa kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.